in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tasirin babban zaben Najeriya na bana ga makomar kasar
2015-02-12 16:43:02 cri

Sakamakon matsalar tsaro da wasu sassan arewacin Najeriya ke fuskanta, ya sa hukumomin tsaron kasar suka baiwa hukumar zaben kasar mai zaman kanta (INEC) shawarar dage zabukan kasar da a baya aka shirya gudanarwa a ranar 14 ga watan Fabrairun shekarar 2015 zuwa ranar 28 ga watan Maris, maimakon ranakun 14 zuwa 28 ga watan Fabrairu. Zabukan da masharhanta da dama ke kallo a matsayin matakin da zai zayyana alkiblar kasar nan da shekaru da yawa masu zuwa.

Yayin da aka dage zaben na Najeriya da tsawon makonni 6, masharhanta da dama na kallon babban zaben kasar a matsayin wata alkibla da za ta fayyace makomar kasar a fannoni da dama. Ciki hadda muhimman batutuwan da a koda yaushe ke bakin 'yan kasar da ma sauran masu fashin baki na ketare; kamar batun tsaro, matsalar cin hanci da rashawa dake addabar kasar, tabarbarewar ababen more rayuwa, karancin ayyukan yi da matasa kasar ke fuskanta, fatara duk kuwa da kasancewar Najeriyar a sahun gaba a karfin tattalin arziki da yawan al'umma a nahiyar Afirka.

Ko shakka babu, batun shawo kan matsalar tsaro da rashin aiki yi,karancin kayayyakin more rayuwa,cin hanci da rashawa da sauran muhimman fannoni da ake fama da su a kasar ta Najeriya za su kasance manyan kalubale da sabuwar gwamnatin dake tafe za ta fuskanta.

Bugu da kari sakamakon wannan zabe zai taka muhimmiyar rawa ga makomar ta Najeriya, musamman a fannin kokarin hadin kan 'yan kasar.

Ana ganin cewa Najeriya kasa ce da ke da yankuna da addinai da kabilu daban-daban. Rarrabuwar kawuna da ake samu tsakanin 'yan kasar ta fuskar kabilanci da kuma addini sun taka muhimmiyar rawa wajen haddasa rikice-rikice a lokuta daban daban.

Masu fashin baki na fatan, hukumar zaben kasar za ta bayyana duk wanda al'ummar kasar suka zaba ba tare da la'akari da yadda kowa ne dan takara ya fito ba, yayin da su kuma masu zabe za su kasance masu bin doka da oda a lokacin zabe da kuma bayan zaben ta yadda kasar ta Najeriya za ta ci gaba da kasancewa kasa daya al'umma daya. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China