in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sojojin ruwa mata da suka fito daga kabilar Uygur karo na farko a kasar Sin
2015-02-03 16:16:38 cri

Kwanan baya, an shirya wani bikin kammala karatu, inda aka yaye wata jami'ar sojin ruwa 'yar kabilar Uygur ta farko a nan kasar Sin, shin wace ce wannan baiwar Allah? Sai ku biyo mu cikin don jin karin bayani cikin wannan shiri.

A wata rana da safe ne cikin tsakiyar watan Yuli na bara, aka shirya wani bikin kammala karatu a kwalejin horas da sojin ruwa na birnin Dalian da ke nan kasar Sin.

"Dily Umar wadda ta zo daga sashen horar da kwararrun jami'ai—"

Dily Umar ta karbi takardar shaidar kammala karatunta yayin da ake kide-kiden soja daga shugaban kwalejin, inda a wannan lokaci ta kafa tarihi na zama jami'ar sojin ruwa 'yar kabilar Uygur ta farko a nan kasar Sin.

Dily Umar Ablet tana daya daga cikin sojojin ruwa mata na farko da suka fito daga kabilar Uygur, wadanda aka zabo daga jihar Xinjiang mai cin gashin kanta a nan kasar Sin, kana soja daliba. Dili Umar tana alfahari da matsayinta na zama jami'ar sojan ruwa 'yar kabilar Uygur ta farko ta kasar Sin.

"Dukkan mu sojojin ruwa mata na farko ne daga kabilar Uygur, ba a taba ganin irin wannan ba a tarihin kasarmu. Na samu horo na tsawon watanni goma a nan, inda na koyi kwasa-kwasai sama da 20. Yabon da na samu ya sanya ni, da takwarorina, har ma da jihar Xinjiang baki daya muke cike da fatan alheri kan makomar mu a nan gaba."

Ita dai Dily Umar, yarinya ce mai shiru-shiru, amma a zuci abin ba haka ba ne. Canjin matsayin da ta samu daga ma'aikaciyar soja zuwa jami'a, ba abu ne mai sauki ba, domin ta fuskanci wahalhalu da dama.

A watan Disamba na shekarar 2011ne Dily Umar, ta kammala karatunta a jami'ar jihar Xinjiang, a kuma wannan lokaci ne rundunar sojin ruwa ta kasar Sin a karon farko ta nemi sojojin ruwa mata daga kabilar Uygur a jihar Xinjiang. A lokacin da ta samu wannan labari, Dily Umar ta yi farin ciki sosai. Saboda mahaifinta tsohon soja ne wanda da ya taba aikin tsaron kan iyaka, saboda aikin da mahaifin nata ya yi a baya,tun tana yarinya Dily Umar ta tsaida kudurin cewa,idan ta girma ita ma za ta shiga aikin soja .

Amma, mahaifin nata ya nuna damuwa cewa, garinsu yana kusa da Hamada, kusa da kan iyaka, amma wurin da 'yarsa za ta je karatu yana bakin teku, kuma wurin birni ne, ko 'yar tasa za ta iya dacewa da wannan babban canji, ko a'a?

Dily Umar ta gaya wa mahaifinta cewa, "ni da kaina na zabi wannan aiki, ba zan yi dan dana sani kan wannan zabi ba ko da zan fuskanci wahalhalu a nan gaba." Wannan kalami da Dily Umar ta yi, ya taimaka mata wajen samun amincewa daga mahaifinta.

Amma, bayan da Dily Umar ta shiga rundunar soja, ta sha wahala sosai a lokacin da ta ke samun horo, har ma ta taba tunanin watsar da aikin domin ta koma gida.

"A duk lokacin da na tashi daga barci da safe, ina jin duk jikina yana ciwo sosai har ma ba na iya tsayawa. A wasu lokutan ma mu sabbin sojoji mu kan ce, me ya kawo mu nan? Don mu sha wahala? Amma, daga baya wasu tsoffin sojoji sun karfafa mana gwiwa, musamman ma mun samu kwarin gwiwa daga wajen iyayenmu. A karshe dai na samu nasanar kawar da wannan matsala."

Daga jihar Xinjiang mai nisa zuwa nan birnin Dalian dake bakin teku, wannan yarinya da ba ta taba ganin teku ba ta soma aikinta na farko a babban jirgin ruwar daukar jiragen saman yaki mai suna Liaoning, wanda ya kasance jirgin ruwa na farko a nan kasar Sin, inda Dily Umar ta taba shiga wasu manyan ayyuka, ciki har da aikin sarrafa babban jirgin, da yin gwajin zirga-zirga da dai sauransu. A shekarar 2013, sakamakon kwarewarta da kuma yadda ta ci jarrabawa mai wahala da aka yi mata, sai aka gabatar da sunanta a cikin jerin sojoji dalibai da za a yiwa karin girma, daga baya kuma ta fara samun horo a kwalejin koyon tukin jiragen ruwan soja na birnin Dalian na tsawon shekara daya. Dily Umar ta bayyana cewa,

"A ganina, da farko ya kamata na gudanar da aiki na yadda ya kamata, gudanar da ayyukan dake gaba na, da kuma zama abin koyi ga sabbin sojoji, wadannan sune abubuwa mafi muhimmanci a yanzu haka."

Kamar yadda Dily Umar ta fada, gaskiya ta zama abin koyi ga sojojin ruwa mata na kabilar Uygur. Ilyna Ekbe ta shiga rundunar soja a lokacin guda da Dily Umar. Yanzu tana karatu a kwalejin koyin tukin jiragen ruwan soja na Dalian, kuma burinta shi ne, zama jami'ar sojojin ruwa kamar Dily Umar.

Ilyna Ekbe wadda ta fito daga garin Karamay, tun tana yarinya ta ke fatan zama likita, saboda tana son sanya tufaffi masu launin fari da likitoci ke sakawa. Ko da yake ba ta cimma wannan buri ba, amma yanzu tana sanya tuffafin sojan ruwa mai launin fari. A ganinta, wannan aiki ya sanya ta jin alfahari, saboda nauyin dake kanta na kiyaye tsaron kasarta.

"Tun ina yarinya na ke son sanya tuffafi masu launin fari, a yayin da nake karatu a jami'a, na samu labarin cewa, ana bukatar sojojin ruwa. Ina ganin, idan na zama sojan ruwa zan iya sanya tuffafi masu launin fari. Ko da yake ba kamar zama likita ba ne da baiwa mutane jinya, amma idan har na zama sojan ruwa zan iya ba da kariya ga kasarmu baki daya, hakika wannan ya sanya ni kara jin farin ciki."

Domin girmama al'adun gargajiyar kabilar Uygur, kwalejin koyon tukin jiragen ruwan soja na Dalian ya kafa wani dakin cin abinci na musamman na halal ga daliban kananan kabilu. Ban da wannan kuma, a yayin bukukuwan gargajiya na kabilar Uygur kamar su Rozah, da babbar sallah, kwalejin ya kan shirya musu bukukuwan nuna fatan alheri na musamman.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China