in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya ta alkawarta gudanar da zabe lami lafiya
2015-01-24 19:49:25 cri
Ministan harkokin wajen tarayyar Najeriya Aminu Wali ya ce mahukuntan kasar na daukar dukkanin matakan da suka wajaba, don ganin an gabatar da babban zaben kasar lami lafiya. Wali ya ce gwamnatin kasar mai ci, za ta tabbatar da gudanar sahihin zabe cikin watan Fabarairun dake tafe kamar dai yadda aka tsara.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da wakilin musamman na babban magatakardan MDD game da harkokin Afirka da Najeriya Mohammed Ibn Chambas. Yana mai cewa yarjejeniyar baya bayan nan da daukacin 'yan takarar kujerar shugabancin kasar suka rattabawa hannu, daya ce daga matakan da ake dauka, na tabbatar da gudanar zaben cikin kyakkyawan yanayin tsaro da kwanciyar hankali.

Kaza lika Wali ya ce gwamnati za ta tabbatar da tsaro, a jihohin Arewa maso Gabashin kasar, inda hare-haren kungiyar nan ta Boko Haram suka fi kamari y yin zabukan na bana.

Daga nan sai ya yi kira ga MDD da ta tallafawa Najeriyar, duba da cewa rashin daukar matakan da suka dace, na iya jefa daukacin yankunan dake yammacin nahiyar Afirka cikin wani mawuyacin hali.

Kafin hakan dai Mr. Chambas ya bayyana cewa Najeriya kasa ce dake da matukar muhimmancin a yammacin Afirka da ma duniya baki daya, don haka ya wajaba a ba ta dukkanin kulawar da ta dace. Ya ce Najeriya na taka muhimmiyar rawa wajen ayyyukan wanzar da zaman lafiya a yankunan nahiyar da dama, wanda hakan ne ya sanya duniya maida hankali game da zaben kasar.

Ibn Chambers ya kara da cewa babban magatakardan MDD, da kwamitin tsaron majalissar na da burin gabatar da laifukan yaki da kungiyar Boko Haram ke aikawa, gaban kotun hukuntan manyan laifuka ta ICC. (Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China