Kasar Somaliya da Kungiyar hadin kan Afrika ta AU sun yi Allah wadai da wani hari da aka aiwatar a kan wani otel dake Mogadishu, babban birnin Somaliya, wanda ya haifar da asarar rayukan mutane 5, tare da haddasa raunata wasu mutane da dama.
Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud wanda ya ziyarci otel din SYL inda aka kaddamar da farmakin ya bai wa wata tawagar kasar Turkiyya dake otel din tabbaci cewar, gwamnatinsa za ta ci gaba da samar da tsaron da ya dace domin maido da zaman lafiya.
Shugaban na Somaliya ya kuma ce, harin ta'addanci da kungiyar Al-Shabaab ta kai ba zai haramtawa gwamnatinsa dakatar da shirin da take da shi na zama mai masabkin baki ga shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan wanda aka shirya zai kai ziyara kasar ta Somaliya a ranar Juma'a.
Ya ce, gwamnati ta tsaurara matakan tsaro a ciki da zagayen birnin domin tabbatar da nasarar ziyarar shugaban kasar Turkiyya.
Ana sa ran, shugaban kasar na Turkiyya zai isa kasar a yau Juma'a domin aiwatar da ziyarar shi karo na biyu a kasar tun bayan zuwan shi kasar a shekara 2011 a lokacin yake rike da mukamin firaminista na kasar Turkiyya.
Tuni dai kungiyar Al-shabaab ta dauki alhakin kaddamar da harin a inda kakakinta Abdiaziz Abu Musab ya ce, sun kai harin ne domin kawo cikas ga ziyarar da aka shirya shugaban kasar na Turkiyya zai kai kasar ta Somaliya. (Suwaiba)