Kamar yadda aka yi a kullum, kwanan baya, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya kai ziyararsa ta farko ta wannan shekara, inda ya ziyarci kasashen Kenya, Sudan, Kamaru, Equater-Guinea, da Kongo(kinshasa), tare da ganawa da takwarorinsa na wadannan kasashe, da shugabannin wadannan kasashe, an ce, ziyararsa za ta karfafa dangantakar da ke tsakanin kasashen Sin da Afrika.(Bako)