in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na shirin karkata ga noman Dankalin-Turawa
2015-01-15 20:19:30 cri


A kwanakin baya ne hukumomin kasar Sin suka yanke shawarar mayar da hankali kan noma Dankalin-Turawa a matsayin daya daga cikin manyan abinci yau da kullum da za a rika ci a kasar, baya ga shinkafa da alkama da masara da hatsi da suka kasance manyan abincin yau da kullum na al'ummar Sinawa.

Bayanai na nuna cewa, Sinawa sun shafe kusan shekaru 400 suna noma Dankalin-Turawa a filayen da suka kai eka miliyan biyar, amma bisa wannan sabon tsari za a bukaci a kalla eka miliyan 120 domin cimma wannan burin na noma Dankalin-Turawa a matsayin daya daga cikin manyan abincin yau da kullum da za a rika ci a kasar.

Sinawa dai sun shafe dubban shekaru suna cin Shinkafa da Alkama Da Masara a matsayin abincinsu na yau da kullum. Kuma an dauki wannan mataki na noma Dankalin-Turawa ne saboda kokarin da kasar Sin ke yi na daidaita tsare-tsarenta na aikin gona da kiyaye hanyoyin samar da isasshen abinci ga al'ummar kasar.

Alkaluman ma'aikatar aikin gona ta kasar Sin na nuna cewa, ya zuwa shekarar 2020, ana saran cin kashi 50 cikin 100 na Dankalin-Turawan da aka noma a kasar a cikin gida.

Bugu da kari bincike ya nuna cewa, a shekarar 2020 kasar Sin za ta bukaci karin kilogram biliyan 50 na abinci saboda karuwar yawan al'umma. Sannan sakamakon karancin gonaki da matsalar canjin yanayi da sauran batutuwa, zai yi wuya a kara yawan Shinkafa da Alkamar da ake nomawa.

Wannan ya sa masana suka mayar da hankali kan batun noma Dankalin- Turawa.

Har ila bincike ya nuna cewa, Dankali yana iya jure fari da sanyi da wasu nau'o'I na matsalar sauyin yanayi, sannan za a iya noma shi a kudancin kasar ta Sin a lokacin sanyi, baya ga amfani mai yawa da za a samu a filin noma kadan, kuma ba ya bukatar ruwa mai yawa ko wasu tsarabe tsarabe.

Masu fashin baki na ganin cewa, wannan mataki na kasar Sin, zai kara samar da abinci ga al'ummar kasar cikin sauki. (Ibrahim/Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China