in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ba a samu bullar Ebola ba cikin kwanaki 44 a kudancin Saliyo
2015-01-13 10:28:10 cri

Rahotannin daga Freetown, babban birnin kasar Saliyo ya nuna cewa, gundumar Pujehun a kudancin Saliyo ya dauki kwanaki 44 ba tare da samun sabuwar bullar cutar Ebola ba, kamar yadda shugaban gundumar Sadiq Siilah ya sanar a ranar Litinin.

Sadiq Siilah yana jawabi ne ga masu ruwa da tsaki daga gundumar wadanda aka gayyato domin su duba wannan sabon ci gaba na tsaikon bullar cutar da aka samu tun lokacin bayyanansa na karshe.

Ya danganta wannan ga nasarar da aka samu a kan kokarin bangaren tsaro, da suka hada da 'yan sanda da sojoji wadanda suka samar da tsaron dakunan gwaji da sha magani da duba masu dauke da cutar, har ma da wuraren bincike na kan hanyoyi da bakin iyakar shiga kasar daga Liberiya.

Alkalumma sun nuna cewa, tun barkewar cutar a gundumar a watan Agustan bara, an samu wadanda suka kamu da cutar su 31, sannan ya zuwa ranar 26 ga watan Nuwamban baran shi ne karo na karshe da aka samu bullar cutar a gundumar.

A wani labarin kuma kamar yadda bayanai na ci gaba suka nuna daga ma'aikatar kiwon lafiyar kasar, daga cikin gundumomin 14 na siyasa a Saliyon, guda 6 ne kadai aka samu, har yanzu da sauran bullar cutar da suka hada da babban birnin kasar Freetown. Sauran 8 din babu sauran rahoton haka tun fiye da makonni biyu ke nan. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China