Gwamnatin kasar Zambia ta kare yadda kamfanin dillancin labaran kasar (ZANIS) game da yadda ya tallafa 'yan takarar shugabancin kasar da za su fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasar da za a gudana ranar 20 ga watan Janairu, bayan da jama'a suka soke shi da nuna son kai.
Hukumar zaben kasar (ECZ) ta bayyana cewa, kamata ya yi ko wane 'dan takara ya ci gajiyar tsarin, amma salon tallafa 'yan takarar da kamfanin dillancin labaran kasar ya yi amfani da shi ya taimaka wa Lungu fiye da sauran 'yan takara.
Ko da yake kakakin gwamnatin kasar Joseph Katema ya karyata zargin da hukumar zaben kasar ta yi cewa, tsarin ya karya dokar zabe. Sai dai tsarin mulkin kasar ta Zambia ya baiwa shugaba mai ci da mataimakinsa ne ikon amfani da kayayyakin gwamnatin a lokacin yakin neman zabe.
Kimanin 'yan takara 11 ne ake sa ran za su fafata a zaben shugaban kasar na ranar 20 ga watan Janairu, sakamakon mutuwar shugaba Micheal Sata ranar 28 ga watan Oktoba. (Ibrahim)




