Shugaban kasar Tanzaniya Jakaya Kikwete ya kori a ranar Litinin madam Anna Tibaijuka, ministarsa dake kula da fadin kasa, gidaje da cigaban jama'a, bayan wata harkar cin hanci ta shafi gwamnatinsa a bangaren makamashi.
Wannan ministar ya kamata ta janye domin mu zabi wani mutumin da zai maye gurbinta, in ji shugaba Kikwete a cikin wani jawabinsa zuwa ga 'yan kasar da aka watsa kai tsaye a gidan talabijin na wannan kasa dake gabashin nahiyar Afrika.
Shugaban kasar ya mai da martani ne bisa shawarwarin majalisar dokokin kasar a cikin watan Nuwamba bayan wani binciken kwamitin 'yan majalisu da ya gano cewa, kimanin dalar Amurka miliyan 120 aka fitar daga aljihun gwamnati, kuma aka zuba wa wani kamfani a bangaren makamashi, sannan kuma aka rarrabawa wasu ministocin gwamnati. (Maman Ada)