in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Afrika ta kudu zai kawo ziyarar aiki kasar Sin mako mai zuwa
2014-11-27 20:43:50 cri
Shugaban kasar Afrika ta kudu Jacob Zuma zai kawo ziyarar aiki a nan kasar Sin daga ranar Laraba mai zuwa zuwa Asabar, kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Hua Chunying ta sheda ma manema labarai a Alhamis din nan.

Wannan ne ziyarrar Zuma ta farko tun sake hayewa karagar mulkin kasar a zagaye na biyu.

A cewar Madam Hua, lokacin ziyarar, Jacob Zuma zai gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping da Firaministan kasar Li Keqiang da shugaban majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang.

A cikin batutuwan da shugabannin zasu tattauna akwai batun zurfafa dangantakar dake tsakanin sassan biyu da sauran batutuwan da suke janwo hankalan bangarorin biyu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China