in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar Sin ya gana da shugaban majalisar wakilan Habasha
2014-11-06 20:48:35 cri
A yau Alhamis 6 ga wata, shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin Zhang Dejiang ya gana da shugaban majalisar wakilan kasar Habasha, Abadula Gemeda, a babban dakin taron jama'a.

A lokacin ganawar, Mr. Zhang ya ce, Sin za ta ci gaba da zurfafa hakikanin hadin gwiwa a tsakaninta da Habasha a duk fannoni, da bunkasa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu.

A nasa bangare, mista Abadula ya bayyana cewa, Sin ta taimaka wa Habasha a fannoni daban daban, don haka Habasha na fatan za a kara bunkasa dangantaka tsakanin kasashen biyu, tare da samun fasahohi daga kasar Sin a fannonin kafa dokoki, gudanar da harkokin kasa da dai sauransu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China