141106-Kasar-Sin-za-ta-tura-masu-horar-da-maaikatan-kiwon-lafiyar-alumma-a-ketare-don-yakar-Ebola-Bello.m4a
|
Zuwa yanzu kasar Sin ta riga ta tura likitoci 252 zuwa kasashen 3 inda yanayin annobar Ebola ya fi tsanani wato Guniea, Laberiya, da Saliyo. Kana kasar Sin na shirin kara tura wasu kwararrun da yawansu zai kai dubu 10 zuwa wadannan kasashe, kuma bisa mataki daban daban. Daga cikinsu, tawagar farko da za ta tashi a wannan karo na kunshe da mutane 12, wadanda suka hada da kwararru a fannonin kwayoyin cuta, ciwon Sida, hana yaduwar cututtuka, da likitoci 2. Za su yi amfani da wata makarantar dake Freetown na kasar Saliyo a matsayin cibiyarsu, inda za su horar da ma'aikatan jinya na kasashen dake fama da cutar Ebola. A cewar shugaban kungiyar kuma mataimakin darektan cibiyar hana yaduwar cututtuka ta kasar Sin, mista Liang Xiaofeng, ban da aikin horaswa, aikinsu ya shafi bangarori masu muhimmanci guda 2,
'Za mu yi bincike kan yanayin da wadannan kasashe suke ciki, da lura da niyyarsu. Abin da suka rasa, shi ne abin da za mu ba su. Yanzu mun san cewa, babu isassun ma'aikatan kiwon lafiyar al'umma da za su gudanar da aiki a ungwanni daban daban. Haka kuma mutanen da suka hada da shugannin addinai, ma'aikatan dake aiki a cikin ungwanni daban daban, da masu aikin sa kai, kusan dukkansu ba su san fasahar maganin cutar Ebola sosai ba. Kana makasudi na biyu shi ne tawagarmu za ta gwada fasahar horaswa, don sanin ta yaya za mu zabi wadanda za su dace da samun horaswa, kuma ko za a iya fahimtar bayanin da muka samar irin na Turanci. Fasahohin da za mu samu a wadannan fannoni za su yi amfani a lokacin da za a gudanar da wasu ayyuka a nan gaba.'
An yi shirin gama aikin horaswa cikin watanni 4 zuwa 6, inda za a horar da likitoci, shugabannin ungwanni, jami'an gwamnati, dalibai, ma'aikatan jinyar jama'a, da masu aikin sa kai, wadanda yawansu zai kai dubu 10. Bayan da wannan tawaga ta tashi, za a tura wasu kwararrun binciken cututtuka a karo na 2. A cewar mista Liang, tallafin da kasar Sin ta bayar a wannan karo yana da ma'ana sosai.
'A da muna da tawagogin likitoci wadanda suka taimakawa jinyar jama'a a kasashe daban daban. Sai dai yadda muka tura mutane da yawa kamar haka don tallafawa aikin kiwon lafiyar al'umma na sauran kasashe ya kasance karo na farko ne, kuma hakan na da ma'ana sosai. A wasu kasashen dake tasowa, babu asibitoci masu inganci da kwararrun likitoci. Annobar da ake fama da ita a wannan karo babu fasahar jinya mai kyau gare ta, don haka mataki kawai da za a iya dauka shi ne kebe wadanda suka kamu da cutar. Amma wadannan kasashe ba su da fasaha a wannan fanni, musamman ma a cikin ungwanni. Lamarin da ya sha bamban da yanayin da kasarmu take ciki a lokacin barkewar annobar SARS. A lokacin idan an samu wanda ya kamu da cutar a wani wuri, to, za a ga jami'an gwamnati da masu aikin sa kai na ungwannin sun fara aiki nan take. Haka zalika, aiki ya fara daga shekarun 1970, kasarmu ta horar da likitocin wadanda suke gudanar da aiki a kauyuka da yawa. Su wadannan likitoci sun taimaka wajen warware matsaloli da yawa. Don haka muna son taimakawa wadannan kasashe samun likitocin da za su yi aiki a ungwanni da kauyuka, hakan kuma zai bukaci dogon lokaci.'
A nata bangare, babbar darektar kwamitin lafiya da kayyade haihuwa na kasar Sin madam Li Bin ta ce, a wannan karo tawagar ma'aikatan kiwon lafiyar al'umma ta kasar Sin za ta tashi zuwa Afirka don koyar da fasahohin kasar a fannin lura da lafiyar jama'a da tinkarar cututtuka masu yaduwa, hakan ya nuna cewa, kasar Sin ta sauya manufarta wajen ba da tallafi, wanda a da ya shafi samar da kudi da kayayyaki ne kawai, amma yanzu sai ta fara tallafawa kokarin tinkarar annoba bisa hanyoyi daban daban.
Ban da haka kuma, dangane da tambayar da aka yi cewar, ko akwai masu dauke da cutar Ebola da suka shigo kasar Sin, mista Song Shuli, kakakin kwamitin lafiya da kayyade haihuwa na kasar Sin ya ce, yanzu babu mutanen da suka kamu da cutar cikin kasar Sin, sai dai ya kasance da hadari na samun wasu masu dauke da cutar da su shigo cikin kasar Sin, don haka hukumomin kasar sun riga sun dauki matakan share fage don tinkarar yanayin ta-baci da ka iya faruwa. (Bello Wang)