in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake bude ofishin jakadancin kasar Sin a Somaliya
2014-10-13 11:31:23 cri

An sake bude ofishin jakadancin kasar Sin a birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya, a ranar Lahadi 12 ga wata, inda mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin mista Zhang Ming, da shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud suka cire kyallen dake alamanta bude ofishin.

A karshen shekarar 1990, yakin basasa ya barke a kasar Somaliya, abin da ya tilasta ma ma'aikatan ofshin jakadan kasar Sin, da wasu likitoci da injiniyoyi Sinawa janye jiki daga kasar a watan Janairun shekarar 1991. Sai dai yanzu shekaru 23 sun wuce, kasar Sin ta sake bude ofishin jakadancinta a Somaliya. Hakan a cewar mista Zhang Ming, ya kasance wani lamari mai muhimmanci da ya faru tsakanin kasashen Somaliya da Sin, wanda ya alamanta cewa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu zai shiga wani sabon mataki. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China