Li Jin ya bayyana cewa, bayan da tawagar likitocin Sin ta isa kasar Saliyo, sun fara gudanar da ayyukansu ba tare da bata lokaci ba. A halin yanzu, sun kammala ayyuka da dama, ciki har da kyautata tsarin asibitin sada zumunta dake tsakanin Sin da Saliyo cikin sauri ta yadda zai iyar karbar mutanen da suka kamu da cuttuttuka masu tsanani dake yaduwa, da tsara ka'idojin karbar mutanen dake fama da cutar Ebola, da kyautata ayyukan ba da jinya, da tsara matakan maganin masu fama da cutar, da kuma horar da likitocin kasar Saliyo a fannonin sanya da cire tufafin maganin cutar da sauran ayyuka makamantan haka.
Li Jin ya kara da cewa, yanzu ana fuskantar matsaloli da dama kan yaki da cutar Ebola a kasar Saliyo, kamar su rashin cikakken tsarin kiwon lafiya na kasar Saliyo da kuma rashin samun cikakkun likitoci dake kwarewa wajen yaki da cuttuttukan dake yaduwa. A yayin da aka gudanar da kamfen takaita fita a dukkan kasar daga ranar 19 zuwa 21 ga wata, mutane da dama sun tsaya gidajensu da karbar binciken da aka yi musu.
Jakadan kasar Sin dake kasar Saliyo Zhao Yanbo ya bayyana cewa, wannan tawagar likitoci ta kasar Sin da ta tashi zuwa kasar Saliyo ta hada da mutane 59. (Zainab)