in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Aikin jigilar Alhazai a nan kasar Sin
2014-09-25 16:27:16 cri

Aikin hajji daya ne daga cikin shika-shiken musulunci nan guda biyar da ake son musulmi ya yi sau daya a rayuwarsa idan yana da hali.

A nan kasar Sin dake da miliyoyin musulmi kamar sauran kasashe da mutanen suke zuwa aikin hajji, ta kan shiryawa alhazanta jirage da masaukai da tawagar likitoci da masu dafa abinci da sauran ma'aikata masu yi musu hidima tun daga nan gida har zuwa kasar Saudiya da kuma dawowa gida.

Baya ga maniyata dake zuwa aikin hajji karkashin hukuma, akwai kuma masu zuwa ta jirgin yawo ko kamfanoni masu zaman kansu.

Sai dai duk da kasancewar hukumomin kula da harkokin alhazai da kasashe ke kafawa da nufin saukaka ayyukan hajji ga al'ummominsu a wasu kasashen hakan ba ya samu wa.

Yayin da sauran maniyatta daga sassan duniya ke haramar sauke aikin Ibada, su ma maniyatan Sin kimanin sama da 14,000 da za su halarci aikin hajjin na bana sun fara tashi daga sassan kasar Sin dabam-daban tun a ranar 4 ga watan Satumba inda ake saran za su dawo gida ranar 10 ga watan Oktoba bayan kammala aikin hajji kamar yadda aka tsara.

Rahotanni na cewa, yanzu haka gwamnatin kasar Saudiyya ta kafa wasu tashoshin binciken lafiyar maniyata don magance shigar cutar Ebola cikin kasar.

Masu sharhi na ganin cewa, wajibi ne kasashe su fito da tsare-tsare da suka dace don kaucewa irin matsaloli da wahalhalu da maniyatta ke fuskanta a shirye-shiryen tafiya aikin hajji da kuma lokacin da alhazai ke kasa mai tsarki. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China