Kuma bisa labarin da ma'aikatar kiyaye zaman lafiyar jama'a ta kasar Sin ta fitar, an ce, haduwar kurar karafa da wuta ce ta haddasa fashewar a masana'antar.
Kaza lika, a yau Asabar 2 ga wata, bisa umurnin shugaban kasa Xi Jinping da firaminista Li Keqiang, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin Wang Yong da wasu jami'an hukumomin gwamnati da abin ya shafa sun isa wurin da wannan hadari ya faru cikin gaggawa domin jagorantar ayyukan ba da agaji da wasu ayyukan makamantan haka na gaggawa. (Maryam)