in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kashe mutane 4 a harin da aka kai a fadar shugaban kasa a Mogadishu
2014-07-10 10:19:48 cri

Ministan yada labarai na kasar Somaliya, Mustaf Sheikh Ali Duhulow ya ce, an kashe wasu 'yan tsagera guda ukku, da wani sojan gwamnatin Somaliya, bayan wani harin da aka kai a fadar shugaban kasar Somaliya, dake birnin Mogadishu.

Ministan yada labaran ya bayyana cewar, wasu 'yan tsagera guda hudu, sun yi kokari su kutsa kai cikin wani babban gini da ya kunshi ofisoshin ma'aikatu dabam-dabam, to amma nan take sai rundunar sojojin Somaliya da sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika AU suka dakatar da maharan.

Maharan sun yi amfani da bam mai ya tashi a mota, da kuma ruwan harbin bindiga a yayin da suka kai farmakin. Kungiyar musulmai 'yan tsagera sun dauki alhakin kai harin.

Sai dai kuma lokacin da aka kai harin, shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamoud, da firaministan kasar Abdiweli Sheikh Ahmed, ba su cikin fadar shugaban kasar. (Suwaiba)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China