in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guinea ta cimma wata dokar yaki da tallafawa ta'addanci
2014-06-03 10:31:44 cri

Yan majalisar dokokin kasar Guinea sun rattaba hannu kan wata dokar yaki da samar da kudade ga ayyukan ta'addanci, tare da kafa wata cibiyar kasa da za ta rika samar da bayanan kudi (CENTIF), haka kuma cibiyar tana da ikon sanya ido kan shige da ficen kudi, a duk lokacin adadin kudin ya wuce Euro dubu biyar, in ji hukumomin kasar.

Cibiyar CENTIF, ba za ta kasance a matsayin wata hukumar 'yan sanda ba, amma za ta samu wani matsayi makamancin haka, da zai ba ta damar bincike kan asalin kudaden da mutane suke dauke da su, idan suka wuce kudin Guinea miliyan hamsin, kwatankwacin Euro dubu biyar.

Mukasudin cimma wannan doka a kasar Guinea, shi ne na cika sharudan babbar hukumar yaki da halatta kudin haram a yammacin Afrika. Hukumar da shugabanni da gwamnatocin kasashe goma sha biyar na kungiyar ECOWAS suka kafa.

Ko wace kasa, mambar kungiyar tana da irin wannan hukuma da kuma cibiyoyin samar da bayyanan kudi domin yaki da halatta kudin haram da kudaden ta'addanci.

Yankin ECOWAS na fama da barazanar kungiyoyin ta'addanci, tare da karuwar hare-haren ta'addancin kungiyar Boko Haram a Najeriya, da kuma rikicin arewacin kasar Mali. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China