An bude taro karo na uku na dandalin tattaunawa a tsakanin kasashen Sin da Afirka na fannonin hukumomi masu zaman kansu a ranar 12 ga watan nan.
Taron dake gudana a birnin Khartoum fadar gwamnatin kasar Sudan, ya samu halartar manyan masu ruwa da tsaki a wannan fanni. Cikin jawabin da ya gabatar ga mahalarta taron ta kafar bidiyo, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon, ya bayyana goyon bayansa ga manufar kasar Sin, ta inganta hadin gwiwa da kasashen Afirka a fannoni daban daban.
Ban Ki-moon ya kara da cewa, kasar Sin muhimmiyar kawa ce ta kasashen Afirka ta fuskokin cinikayya da neman samun ci gaba. Ya ce ana fatan kasar Sin da kasashen Afirka za su yi amfani da cigaban dangantakar da ke tsakaninsu, wajen inganta hadin gwiwarsu kan batutuwan rage talauci, da yaki da cututtuka, da sauyin yanayi, da kyautata ayyukan gudanarwa da kasashen Afirka ke fuskantawa, domin ba da tabbaci wajen samun daidaito ta fuskar rarraba albarkatun halittun nahiyar.
Bugu da kari Ban Ki-moon ya nanata cewa, MDD za ta ci gaba da goyon bayan kasashen Afirka, a kokarinsu na neman samun bunkasuwa.(Kande Gao)