in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin masu cutar Ebola ya cimma 134 yayin da 84 suka mutu a Guinee
2014-04-03 10:44:31 cri
A cewar hukumomin kiwon lafiya na kasar Guinee, an gano wasu mutane hutu dauke da cutar dake janyo zubar da jini wato Ebola, mutum daya a Gueckedou, kana uku a Macenta, abin da ya kai yawan masu cutar zuwa 134, yayin da mutane 84 suka mutu a wannan kasa dake yammacin nahiyar Afrika tun lokacin barkewar annobar mai kashewa.

Ma'aikatar kiwon lafiya ta Guinee da ta fitar da sabon labari ta bayyana cewa adadin kamuwa da cutar na kusan kashi 63 cikin 100.

Cutar ta rarrabu kamar haka, Gueckedou an gano mutum 80 yayin 58 suka mutu, Macenta mutum 26 yayin da 14 suka mutu, Kissidougou mutane 9 yayin da 5 suka mutu.

Sannan Conakry, babban birnin kasar inda aka gano mutane 15 yayin 4 suka mutu. Haka yankuna dake tsakiyar Guinee wadanda suka hada Dabola an samu mutum 3 yayin da 2 suka mutu, sai kuma Dinguiraye mai mutum guda da mutuwa daya.

Binciken kwayoyin wannan cuta a dakunan bincike ya tattabar da nau'in cutar Ebola 35, in ji ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Guinee.

Bisa kokarin kawar da annoba, an dauki matakai da dama da suka hada da kafa cibiyoyin kebe masu jinya a yankunan da cutar ta fi kamari, sanya magani a gidajen mutanen da cutar ta kashe, bullo da hanyoyin fuskantar wannan annoba, samar da kudade, aike wa da kayayyaki kariya na mutum daya daya da rarraba jakar kayayyakin rigakafi a yankunan da cutar ta shafa.

Haka ma asusun kula da yara kanana na MDD wato UNICEF shi ma ya fara rarraba jakar kayayyakin tsabta a cikin makarantun dake yankunan da cutar shafa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China