in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
A Tanzania an bankado sabuwar hanyar da masu safarar muggan kwayoyi ke bi
2014-02-06 16:41:27 cri
Mahukunta a kasar Tanzania sun ce sun gano dabarar boye muggan kwayoyi cikin halastattun kaya, da masu fataucin muggan kwayoyi tsakanin kasashen Afirka ke bi wajen shigar da hajojinsu.

Mataimakin minista a ma'aikatar sifirin kasar Charles Tizeba ne ya bayyanawa wakilan kwamitin majalissar dokokin kasar mai lura da harkokin samar da ababen more rayuwa hakan, yayin ziyarar aiki da suka gudanar a babban filin tashi da saukar jiragen sama na Julius Nyerere dake kasar.

A cewar Mr. Tizeba, hukumar gudanarwar filin jirgin saman ta samu nasarar damke kaya, da a kan aiko ta sakon gidan waya har kashi 8 cikin mako guda, bayan da aka gano cewa masu wannan muguwar sana'a, su na boye muggan kwayoyi, da ragowar kayan maye cikin nau'o'in kayayyaki daban daban, da suka hada da takalma, da jakukkunan shayi da dai sauransu.

Ya ce a baya bayan nan ma an damke wani kunshi kaya da ake son aika zuwa Namibia, dake dauke da littattafai, wadanda aka boye hodar Heroin a cikin su. (Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China