Ministan tsaron kasar Mali, Soumeylou Boubeye Maiga, ya tabbatar a ranar Lahadi cewa, babu wani batun yarjejeniyar tsaro tsakanin Mali da Faransa a ranar 20 ga watan Janairu, sabanin jita-jitar da ake yadawa kan wannan batu a birnin Bamako.
"Ba mu tsai da ranar 20 ga watan Janairu bisa wannan ba, amma tare da kasar Faransa kamar sauran kasashe, muna ganin ya dace mu samu wani tsarin siyasa da dokoki da za su taimaka wajen shirya dangantaka ta fuskar soja, kamar yadda ake a wasu fannonin ilmi, kiwon lafiya, harkokin kudi da sauran fannoni." in ji ministan a yayin wata liyafar cin abinci tare da 'yan jarida.
Tawagogin kwararru na cigaba da aiki domin bullo wata yarjejeniyar hadin gwiwa ta fuskar tsaro, haka kuma ministan ya nuna cewa, wannan wata dama ce ga farfado da dangantakar tsaro tare da kasar Mauritaniya da kuma wata kila tare da kasar Chadi, kafin ya tunatar da cewa, kasarsa na da irin wannan dangantaka tare da kasashen Nijar da Aljeriya.
Liyafar tare da 'yan jarida, an shirya ta bisa bukukuwan cika shukaru 53 da kafa rundunar sojojin kasar Mali. Haka kuma wata dama domin kaddamar da aikin gine-gine gidan jama'a ga rundunar sojojin kasar.
Ranar 20 ga watan Janairu rana ce mai muhimmanci ga rundunar sojojin kasar Mali, domin a ranar 20 ga watan Janairun shekarar 1961 ne shugaban kasar Mali na farko Modibo Keita ya bukaci kasar Faransa da ta janye sojojinta daga sansanonin da ta kafa a biranen Bamako, Kati, Gao da Tessalit na kasar Mali. (Maman Ada)