in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Malama Wan da cibiyarta ta horar da matan dake kula da renon yara da ayyukan-gida(2)
2013-12-31 15:10:41 cri

Ita dai wannan cibiyar horar da matan dake kula da renon yara da ayyukan gida an kafa ta ne a shekarar ta 2001, yau shekaru 12 ke nan, kuma baya ga aikin reno da kula da gida da wannan cibiya ke samar wa, tana kuma koyar da sana'o'in hannu na musamman ga wadanda aka sallama daga wajen ayyukansu kamar masana'antu domin su samu abin dogaro da kai.

A bangaren koyar da dabarun kula da gida wanda ya shafi girki, shara, goge-goge walau na gida ko kayan cikin gida saboda kura ko lalacewa sakamaon ajiya na tsawon lokaci, wannan cibiya ta horas da mata sama da 1,500 wadanda aka sallama daga wassu ma'aikatu musamman masana'antu da kuma mata da suke zuwa ci rani, wato wadanda suka shigo maraya domin neman na rufin asiri.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China