A ranar Alhamis din nan 5 ga wata, Algeriya ta amince da bukatar da Amurka ta gabatar mata ta son dawo mata da 'yan kasarta guda biyu da ake tsare da su a gidan kurkukun Guantanamo dake kasar Cuba, in ji kafar yada labaran kasar ta Algeriya.
Hukumomin shari'a ne za su kula da wadannan 'yan kasa da ake kokarin dawo da su bisa doka, in ji kamfanin dillacin labaran kasar Algeriya APS.
An ce, wadanda ake tsare da su su ne Bensayeh Belkacem, 'dan shekaru 51 da kuma Djamel Ameziane, 'dan shekaru 46.
Kurkukun Guantanamo na daya daga cikin mallakan sojojin ruwan Amurka a kasar waje wanda ya fi dadewa dake tsakiyan teku a kudu maso gabashin Cuba. Har yanzu, akwai mutane 164 da yawancinsu kuma ba a yi musu caji ba dake tsare.
Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya sha yin alkawurran rufe wannan kurkuku tun a shekara ta 2009, amma ya zuwa yanzu hakan ya ci tura. (Fatimah)




