Yaduwar kwayoyin cutar shan inna ta ragu a Najeriya, in ji asusun kula da kananan yara na duniya wato UNICEF.
Matsalar ta halin yanzu na nuna cewa, Najeriya tana bisa hanya mai kyau domin kawar da yaduwar cutar shan inna, in ji mista Priyanka Khanna, kakakin kungiyar UNICEF a yayin wata ganawarsa tare da 'yan jarida a jihar Kano, hedkwatar da wannan cuta ta fi kamari dake arewa maso yammacin kasar kafin ranar duniya ta shekarar 2013 kan yaki da cutar shan inna da za'a bikinta a ranar Alhamis mai zuwa.
Haka jami'in ya yi amfani da wannan dama domin jaddada cewa, a wannan shekara, yaduwar sabbin kwayoyin cutar ta ragu da kashi 52 cikin 100. Wannan faduwar alkaluma ta biyo bayan sakamakon kokarin da duniya ke yi domin kawar da wannan cuta.
Kasar Najeriya da kuma wasu kasashe biyu wato Pakistan da Afghanistan sun kasance kasashen da har yanzu cutar shan inna take kawo illa a shekarar 2013, in ji kungiyar kiwon lafiya ta duniya. (Maman Ada)