A yayin ganawar, mista Yu ya yi maraba da sarakunan 2 da suke halartar taron baje kolin, ya yi fatan cewa, sakamakon goyon baya daga kasashen Sin da Larabawa, wadanda suke kuma halartar taron cikin himma da kwazo, zai sanya taron baje kolin ya zama wani dandali na gari wajen inganta fahimtar juna a tsakanin kasashen Sin da Larabawa, da karfafa mu'amala da hadin gwiwa a tsakaninsu ta fuskar tattalin arziki da cinikayya, da kuma kara azama kan bunkasuwar bangarorin 2 tare.
A nasa bangaren kuma, sarki Abdullah Bin Hussein II ya ce, kasarsa ta Jordan ta yaba wa manyan nasarorin da kasar Sin ta samu ta fuskar ci-gaba, tana son yin koyi da fasahohin kasar Sin ta fuskar raya kasa, zurfafa hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen 2 a fannoni daban daban, da taka kyakkyawar rawa a cikin kasashen Larabawa, a kokarin raya huldar da ke tsakanin Jordan da Sin da kuma tsakanin kasashen Sin da Larabawa zuwa sabon mataki.
Har wa yau a nasa bangaren, sarki Sheikh Hamad Bin Isa al-Khalifa ya ce, kasarsa ta Bahrain da Sin sun kulla zumunci cikin dogon tarihi, yanzu suna fuskantar kyakkyawar dama wajen karfafa hadin gwiwarsu ta a-zo-a-gani. Burinsa na kawo wa kasar Sin ziyarar shi ne habaka hadin gwiwar moriyar juna a tsakanin Bahrain da Sin, a kokarin ciyar da huldar da ke tsakanin kasashen 2 gaba.(Tasallah)




