in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ranar masoya ta Sinawa
2013-08-27 17:08:21 cri


Sanin kowa ne ranar 14 ga watan Faburairu na kowace shekara rana ce ta masoya a wasu kasashen yammacin duniya. A hakika, ban da Turawa, sauran al'ummomin duniya su ma suna da al'adu na kusa da suka shafi ranar masoya, sai dai ya yiwu a rana ta daban, kuma ta hanyoyi na daban ne ake wannan rana, kuma asalin ranar ma ya yiwu ya bambanta.A nan kasar Sin, a ranar 7 ga wata na bakwai bisa kalandar gargajiya na Sinawa ake wannan biki na ranar masoya.

Ranar masoya na da dogon tarihi a kasar Sin, wadda idan muka bincika muke iya gano asalinta tun lokacin daular Han a shekaru kimanin dubu biyu da suka wuce. Sai dai a lokacin, ba ta da wata nasaba da masoya, a maimakon haka kuma, ana kiranta ranar Qiqiao da Sinanci, ma'ana wato ranar da mata ke rokon ubangiji ya ba su hikima da kwarewa wajen fasahohin gida, sabo da kwarewa wajen gudanar da harkokin gida ta kasance abin wajibi ga mata a wancan lokaci. Sabo da haka, a da a lokacin wannan rana, mata su kan ajiye 'ya'yan itatuwa masu kyau, don rokon ubangiji ya ba su kwarewar gudanar da harkokin gida, da kuma aure mai kyau.

To ke nan tun farkon fari, wannan rana ce da mata ke rokon kwarewar fasahohin gida, babu nasaba da soyayya. Al'ummar kasar Sin sun dauke ta a matsayin ranar masoya ne a sakamakon wata almara, wadda a nan kasar kusan babu wanda bai san ta ba. Almaran ta nuna cewa, sauraniyar aljannar duniya na da 'ya'ya mata bakwai, kuma 'yar autarta wadda ake kira Zhi Nu tana da kyaun gani da kuma basira sosai. Kowace rana, tana kokarin sakawa a aljanna, kuma gajimaren da muke gani shi ne abin da take saka. Sai kuma a duniyar 'yan adam, akwai wani saurayi mai suna Niu Lang wanda ke ban tausayi sosai. Maraya ne shi, wanda ba shi da kome sai dai wata saniyar da yake kiwo. Wata rana, saurayin ya yi kuka a kan rayuwarsa, sai saniyar ta ba shi hakuri, ta ce, za ka samu mata mai kyau. Bisa ga yadda saniyar ta nuna masa, saurayin ya je wani kogi da dare, inda 'ya'ya bakwai na sarauniyar aljanta ke wanka, kuma saurayin ya boye rigar 'yar auta da ake kira Zhi Nu. Da 'ya'yan sarauniyar aljanna suka gama wanka za su tafi, 'yar autar ta kasa samun rigarta, kuma kawayenta ba yadda za su yi sai su bar ta a wurin. A lokacin, saurayin ya bullo da rigarta, kuma ya roki Zhi Nu ta aure shi, kuma Zhi Nu ta yarda. To shi ke nan, Niu Lang da Zhi Nu suna zama tare cikin jin dadi da walwala sosai, har suka haifi yara biyu. Amma sarauniyar aljanna ta ji fushi sosai da ta ji labarin auren, har ta umurci a koma da Zhi Nu aljanna. Niu Lang kuma ya yi bakin ciki kuma ya yi kokarin bin matarsa. Ganin haka, sarauniyar aljanta ta cire wata basila daga gashin kanta kuma ta yi amfani da shi ta ja wani layi a tsakanin Niu Lang da Zhi Nu, layin da ya zama wani babban kogi a sararin sama har ya raba Niu Lang da matarsa.

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China