An rufe taron kolin AU karo na 21
|
An rufe taron kolin kungiyar AU, jiko na 21 a ran 27 ga wata a birnin Addis Ababa hedkwatar kasar Habasha. Taron na wannan shekara ya zo daidai da cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika (OAU) wacce ta zamo kungiyar AU, inda hakan ya sa, an mai da muhimmanci sosai kan wannan taro.
An yi gaggarumin bikin taya murnar cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar hadin kan kasashen nahiyar Afrika wacce ta zama kungiyar AU yayin taron mai jigo "Pan-Afrika da farfado da Afrika". Firaministan kasar Habasha Hailemariam Desaleg wanda ke rike da shugabancin karba-karba na kungiyar AU ya yi jawabi a bikin rufe taron na cewa:
"Idan aka waiwayi ci gaba da kalubaloli da muka saba fuskanta a baya, mun sake shan alwashin samun ci gaba bisa tsarin hada kan Afrika. Babban ci gaba da aka samu a cikin taron shi ne zartas da sanarwar kungiyar, abin da ya nuna niyyar da muke dauka ta mai da nahiyar Afrika jiga-jigan duniya"