in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Halin da ake ciki game da tashe-tashen hankula da aka samu a gundumar Bachu da ke jihar Xinjiang na kasar Sin
2013-05-03 16:45:06 cri

Maimaiti Kadir mai shekaru 79 da ya rasa diyarsa Riguli Maimaiti cikin wannan mumunan tashin hankali, yayin da ya tabo maganar mutuwar diyarsa, wannan tsoho ya nuna kiyayya ga masu ta da kayar baya ba tare da rufa-rufa ba, ya ce, "Masu ta da kayar baya sun kashe diyata, kuma makarkashiyar da suka kulla ta bakanta zukatan jama'ar kabilu daban daban, yanzu muna zaman rayuwa mai kyau, me ya sa suka aikata wannan laifi na marasa imani, ba su da iyalai ne? ba su san radadin rabuwa da iyalai ba?

Bisa labarin da manema labaru suka samu, an ce, yayin da wannan lamarin ya auku, sabo da masu tada zaune tsaye sun kunna wuta, gashi kuma an yi saman gidajen wurin da itace, kuma dukkan gidaje a hade suke, sabo da haka, idan gobara ta tashi a wani gida, hakan zai kawo barna ga sauran iyalai. Ko da yake, masu aikin kwana-kwana na wurin sun yi aikin kashe wuta cikin gaggawa, amma duk da haka lamarin ya haddasa rushewar gidajen jama'a da dama, gidaje 6 na Amina Kadir sun rushe cikin gobarar. Ga kuma abin da take cewa,"Yanzu, an kone wadannan gidaje kurmus, jama'a ba za su zauna a ciki ba, na nuna kiyayya ga wadannan mutane, su ne suka kawo barna ga zaman rayuwarmu, ina fatan gwamnati za ta gurfanar da su gaban kuliya."

Bangaren 'yan sanda na jihar Xinjiang ya ba da labari cewa, ya zuwa ranar 28 ga watan Afrilu, an kammala aikin binciken mummunan tashe-tashen hankula da aka samu a ranar 23 ga watan Afrilu, kuma an cafke mambobin kungiyar 'yan ta'adda 25 da ke karkashin jagorancin Qasim Maimaiti da Abby Bula Barat.

Gwamnan jihar Xinjiang ta Uygur mai cin gashin kanta Nur Bekri ya bayyana cewa, tashe-tashen hankula da aka samu a ranar 23 ga watan Afrilu a gundumar Bachu ba zai kawo cikas ga halin da ake ciki a jihar Xinjiang ba, kuma nan gaba, za a inganta matakan rigakafi, don yaki da 'yan ta'adda a wurin. Ya ce, "Na yi imani cewa, wannan lamari ba zai yi tasiri game da yanayin zaman lafiya na jihar Xinjiang ba, kuma za mu inganta matakan rigakafi, don yaki da 'yan ta'adda, da kiyaye zaman lafiya na kabilu daban daban na jihar Xinjiang bisa doka, ta yadda za a tabbatar da tsaro da moriyar 'yan kasar."(Bako)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China