A yayin taron, an ce, dole ne a yi kokarin kara bukatun da ba za su gurbata muhalli ba a kasuwannin cikin gida. Kana dole ne a kara bunkasa tattalin arzikin dake da nasaba da kasuwannin kasashen duniya, kara bude kofofin ayyukan ba da hidima ga kasashen waje, nuna goyon baya ga kokarin zuba jari a kasashen waje kan muhimman fannoni da ayyuka. Sannan dole ne a yi kokarin tabbatar da farashin kayayyaki da kyautata tsarin masana'antu, ta yadda za a iya kara bunkasa sabbin masana'antu masu muhimmanci. Kuma ya kamata a hanzarta neman dabarun magance gurbata muhalli da koguna da ruwan dake karkashin kasa. Bugu da kari, ya kamata a dauki matakan mayar da yankuna masu karkara da su zama garuruwa domin neman ci gaba cikin daidaito tsakanin yankuna daban daban.
Haka kuma, a yayin taron, an jaddada cewa, za a kara yin kokarin kyautata zaman rayuwar jama'a da aikin ceto a yankin da bala'in girgizar kasa na Lushan ya shafa. (Sanusi Chen)