in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Fadar shugaban Afrika ta Kudu na maraba da ziyarar shugaban kasar Sin
2013-03-25 10:33:45 cri

Kasar Afrika ta Kudu na maraba sosai da ziyarar shugaban kasar Sin Xi Jinping, in ji fadar shugaban kasar a ranar Lahadi.

Shugaba Jacob Zuma zai tarbi shugaban kasar Sin Xi Jinping a ranar Talata a cikin wata ziyarar aikin da zai kawo a kasar Afrika ta Kudu, in ji wannan sanarwa.

Shugabannin biyu za su gana a birnin Pretoria, sannan kuma za su sanya hannu kan wasu jerin yarjejeniyoyin hadin gwiwa.

Haka zalika sanarwar ta bayyana cewa, kasar Afrika ta Kudu na son karfafa huldarta tare da kasar Sin a karkashin jagorancin shugaba Xi Jinping, a cewar kamfanin dillancin labaran kasar Afrika ta Kudu Bua a ranar Lahadi.

Kasar Sin ita ce kasa ta farko wajen huldar kasuwanci da kasar Afrika ta Kudu. Ciniki a tsakanin kasashen biyu ya cimma dalar Amurka biliyan 22 a shekarar 2012. A yayin wannan ziyara a kasar Afrika ta Kudu, shugaban kasar Sin zai kuma halarci dandalin tattaunawa na kasashen BRICS wato Brezil, Rasha, Indiya, Sin da Afrika ta Kudu.

Wannan shi ne karon farko da wata kasa dake nahiyar Afrika za ta karbi bakuncin dandalin tattaunawa na kasashen BRICS tun bayan ta zama mamba na wannan gungun kasashen dake tasowa a shekarar 2010. Kasashen BRICS na wakiltar kashi 43 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, suke rike da kashi daya cikin kashi biyar na GDP a duniya tare kuma da kashi 11 cikin 100 na zuba jarin waje kai tsaye. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China