Madam Hua ta kara da cewa, a baya kasashen Afirka sun dade suna shan wahalar mulkin mallaka, dan haka tabbas ne su fahimci ma'anar mulkin mallaka. A shekarun baya, hadin gwiwar da ke tsakanin kasashen Sin da Afirka ta kara azama kan bunkasar tattalin arzikin Afirka da ma kyautatuwar zaman rayuwar al'ummar Afirka, hakan da ya samu amincewa daga kasashen Afirka da duk duniya baki daya. Amma malam Sanusi Lamido Aminu Sanusi ya kwatanta hadin gwiwar Sin da Afirka da mulkin mallaka da kasashen yammacin duniya suka taba yi wa Afirka, lamarin da ba shi da ma'ana. Kasar Sin za ta ci gaba da raya hulda tare da kasashen Afirka, a kokarin ba da gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya, kwanciyar hankali da bunkasuwa a nahiyar ta Afirka, bisa ka'idojin nuna sahihanci da abokantaka, yin zaman daidai wa daida, samun moriyar juna da bunkasuwa tare. (Tasallah)