Shugaban kasar Amurka Barack Obama a ranar Alhamis 17 ga wata ya yi alkawarin aiki da sabuwar gwamnatin Somaliya domin inganta zaman lafiya da tsaro, ganin cewa, gwamnatinsa ta amince da sabuwar gwamnatin dake karkashin jagorancin shugaba Hassan Sheikh Mahamud.
Obama wanda ya yi wannan furucin ne ta bakin mataimakin mai ba da shawara ta fuskar tsaro Denis McDonough a wani ganawa da shugaba Mahamud a fadar gwamnatin Amurka ta 'white house', ya kuma taya shugaban Somaliyar murna dangane da zabensa a wannan matsayi a watan Satumban bara tare da kafuwar wakilin gwamnati na farko a cikin shekaru 20.
Shugaban Amurkan ya jaddada kudirinsa na aiki tare da sabuwar gwamnatin Somaliya don inganta zaman lafiya, tsaro, tafiyar da daburun tattalin arziki da kuma habaka samar da ababen more rayuwa a kasar.
A nata bangaren ita ma sakatariyar harkokin waje Hillary Clinton ta gana da sabon shugaban kasar na Somaliya inda ta sanar da cewa, Amurka ta amince da sabuwar gwamnatin Somaliya, abin da ya kasance na farko tun shekarar 1991.
Shi dai gwamnatin Somaliya ya rushe ne bayan da yakin basasa ya barke, abin da ya ba da dama ga 'yan kungiyar Al-shabaab ta samu karbe daukacin kudanci, tsakiya da ya hada da babban birnin Mogadishu.
Sojojin kasar da kuma na kungiyar tarayyar kasashen Afrika AU sun kwato wadannan wurare bayan bata kashin da aka yi a shekara ta 2011, an rantsar da majalisar dokoki, abin da ya samar da kafuwar sabuwar gwamnati a kasar tun lokacin da aka daina yakin basasa.(Fatimah)




