A cikin sakonsa na taya murna ga Mr. Xi, shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ya lashi takwabin yin aiki kafada da kafada da sabon shugaban na kasar Sin, ta yadda za a bunkasa harkokin cinikayya da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
Shugaban na Najeriya ya ce, gwamnatinsa za ta ci gaba da nuna kulawa da irin taimakon da gwamnatin Sin ke baiwa Najeriya kamar a sassan da suka shafi kayayyakin more rayuwa, makamashi, sufuri da kuma sadarwa.
Shi ma a sakonsa na taya murna, shugaba Mahamadou Issoufou na jamhuriyar Niger, ya ce manufofin JKS, da suka shafi bude kofa ga kasashen waje, sun taka muhimmiyar rawa ga irin nasarorin da kasar Sin ta samu a fannoni daban-daban tare da zama daya daga cikin kasashe masu karfin tattalin arziki a duniya.
Shugaba Issoufou ya bayyana kudurinsa na kara kokarin hada kai da Xi don kara karfafa dankon zumunci da hadin kai tsakanin kasashen biyu da kuma al'ummominsu.
A sakonsa na murna ga Xi Jinping shugaba Bai Koroma na Saliyo kana shugaban jam'iyyar APC, ya ce, "a madadin ni kaina, gwamnati da al'ummar jamhuriyar Saliyo, ina taya ka farin ciki tare da kasancewa cikin koshin lafiya, kuma ina fatan cewa, dankon zumuncin da ke tsakanin kasashen biyu zai ci gaba". (Ibrahim)