in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Afrika sun taya Xi Jinping murna
2012-11-17 17:08:10 cri
Shugabannin kasashen Afrika da na Jam'iyyun siyasa sun aike da sakwannin taya murna ga Xi Jinping bisa ga zabensa a matsayin babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

Goodluck Jonathan, shugaban Nigeriya kuma dan jam'iyyar PDP dake rike da ragamar kasar yanzu, a sakonsa ya ce, zaben Xi ya nuna gudummawar da ya bayar wajen cigaban kasar Sin. Kuma ya nuna cewa, al'ummar kasar sun gamsu da ya jagorance su, Sin za ta kara samun cigaba matuka, kana da bada nata taimako wajen samar da zaman lafiya a duniya. Shugaba Jonathan ya kara da cewa, Nigeriya a shirye take ta yi aiki da Sin a al'amuran duniya domin fuskantar kalubale daga ko wane bangare.

Shi ma a nasa sakon taya murnar, Dioncounda Traore, shugaban kasar Mali kuma shugaban Jam'iyyar Alliance for Democracy ya ce, zaben Mr Xi ya nuna amincewar da Sinawa suka yi masa sakamakon kwarewarsa wajen iya jan ragamar mulki. Don haka, ya jaddada aniyar kasarsa ta Mali ta son cigaba da karfafa abota da hadin gwiwa da kasar Sin.

Shi ma shugaban kasar Guinea Lansana Conte a nasa sakon taya murnar, ya bayyana cewa, kasar Sin za ta cimma wani sabon cigaba ta fannin tattalin arziki, walwalar jama'a da kuma raya al'adu a karkashin shugabancin Xi. Ya nuna imaninsa cewa, Xi zai tsaida kudurin ganin ya ciyar da huldar abokantaka da hadin gwiwa da yanzu haka yake wakana a tsakanin Afrika da kasar Sin.

Ita ma a nata sakon taya murnar, shugabar Unity Party kuma shugabar kasar Liberiya Ellen Johnson-Sirleaf cewa ta yi, gwamnatinta za ta tsaya tsayin daka na akidar kasar Sin daya tak a duniya, kuma za ta yi kokarin hadin kai da kasar ta Sin na ganin ta daukaka mutunta juna da zai amfana wa dukkan bangarori musamman domin cigaban al'ummomin kasashen biyu da ma samar da zaman lafiya da lumana a duniya.

Shi kuma Rui Duarta Barros, firaministan Guinea Bissau a nasa sakon murnar, ya yi ma Mr Xi fatan alheri a sabon matsayinsa da yake yanzu. Ya ce, da shi da gwamnatinsa tun da can sun dauki kasar Sin a matsayin wata babban jigo a kan tubalin cigaba.(Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China