in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
JKS na fatan ganin duniya ta kara fahimtar kasar Sin bisa tsarinta na raya harkokin al'adu
2012-11-16 18:23:06 cri






A 'yan shekarun da suka gabata, kasar Sin ta zama tamkar wata tauraruwa mai walkiya a fadin duniya, sakamakon saurin karuwar tattalin arzikin da ta samu. Amma sabo da rashin sanin al'adun kasar Sin, wasu na gaza fatimtar kasar, musamman ma dimbin baki masu sha'awar kasar. Yayin babban taro karo na 18 na wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka rufe ba da jimawa ba, an mayar da batun raya kasar ta fuskar al'adu a matsayin daya daga cikin burin da kasar za ta nemi cimmawa a nan gaba, tare da nufin yada al'adun kasar ta Sin ta hanyoyi daban daban domin ganin duniya ta fahimci hakikanniyar kasar Sin.

A 'yan kwanakin nan, wannan waka mai taken "Gangnam Style" daga kasar Koriya ta Kudu tana kara shahara kwarai da gaske a duk duniya, hakan ya sa dimbin mutane suka fara fahimtar al'adun kasar Koriya ta Kudu, batun kuma ya zama wani kyakkyawan misali wajen sadarwa tsakanin al'adu daban daban. Wannan lamari shi ma ya sa jama'ar kasar Sin sun yi tunanin cewa, kasancewarta daya daga cikin al'adu na kasashen gabashin duniya, ina dalilin da ya sa irin al'adu na kasar Koriya ta Kudu ke iya haifar da babban tasiri a duk fadin duniya?

A 'yan shekarun nan da suka gabata, dimbin mutanen kasashen waje sun bayyana aniyarsu ta fahimtar kasar Sin, sakamakon saurin karuwar tattalin arzikin ta da kuma karfinta a dukkan fannoni. Domin biyan bukatun wadannan mutane, masana'antar samar da fina-finai ta Hollywood ta kasar Amurka, ta samar da fina-finai da dama da suka shafi al'adun kasar Sin kamar su Hua Mulan, da Kungfu Panda. Amma kasar Sin ita kanta ba ta yada al'adun nata yadda ya kamata, wanda ya sa dimbin baki ba su da masaniya kan al'adun kasar, ballantana ma su fahimce su.

Ge Jianxiong, wani shahararren masani na jami'ar Fudan ta kasar Sin yana ganin cewa, ya kamata aikin raya harkokin al'adu ya dace da matsayin kasar Sin ta fuskar tattalin arziki a duniya. Yana mai cewa,

"A cikin wani tsawon lokaci, kasahen duniya ba su fahimci al'adunmu sosai ba, ya kamata mu kara gabatar da al'adun kasar Sin ga kasashen waje, domin a fahimci al'adunmun namu, da kuma kawar da ricike-riciken da ke tsakanin kasa da kasa sakakamakon rashin fahimtar juna. A matsayinmu na kasar da ke sauke babban nauyi, ba kawai muna taka rawa a fannin tattalin arziki ba ne, a'a ya dace ma mu sa duniya ta kara fahimtar ra'ayoyinmu ta fuskar al'adunmu, da kayayyakinmu, kana da ayyukanmu na ba da hidima."

Domin cimma wannan buri, kasar Sin na aiwatar da babban tsarin "fitar da al'adunta zuwa ketare", wato yada al'adun Sin a duniya ta hanyoyin yin cudanya a tsakanin gwamnatoci, fitar da kayayyakin al'adu zuwa ketare, da kuma yin mu'amala a tsakanin kafofin watsa labaru na gida da na waje. Yanzu kwalejojin Confucius fiye da 390 na koyar da Sinanci a kasashen duniya daban daban, haka kuma an kafa dimbin cibiyoyin al'adun kasar Sin a ketare. A sa'i daya kuma, ta hanyar yin amfani da wadannan wurare, ana nuna al'adun gargajiya na kasar Sin ga duniya, kamar su wasan Alhajin Allah ya kiyaye, wasan Kungfu, fasahar rubutun Sinanci, wasan kwaikwaiyo na Opera, da kuma wasan Taijiquan. Bugu da kari kuma, a idanun Sinawa, samun lambar yabo ta Nobel kan adabi da Mo Yan, wani marubuci Basine ya yi bisa littafin da ya rubuta kan karkarar kasar Sin, ya dada sa duniya ta fahimci kasar.

Sun Zhijun, mataimakin ministan watsa labaru na JKS yana ganin cewa, ana fitar da al'adun kasar Sin zuwa ketare ne domin duniya ta fahimci hakikanin kasar, a matsayinta na kasa da ke neman samun ci gaba da zaman lafiya. Ya kara da cewa,

"Ana fitar da al'adun kasar Sin zuwa ketare ne domin kasashen duniya su kara fahimtar kasar Sin, hakan zai taimakawa kasar wajen samun amincewa daga sauran kasashe, ta yadda za su hada kansu, don neman samun zaman lafiya da ci gaba. Muna dora matukar muhimmanci kan wannan mataki na fitar da al'adun kasar Sin zuwa ketare, domin duniya ta fahimci hakikanin kasar Sin, da ke neman samun ci gaba da zaman lafiya."

A 'yan shekarun nan, JKS da ke kan karagar mulkin kasar tana kara kaimi, a fagen raya harkokin al'adu. A gun babban taro karo na 18 na wakilan Jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin da aka rufe ba da jimawa ba, an mayar da batun raya kasar ta fuskar al'adu don kara karfin kasar a matsayin daya daga cikin burin da kasar Sin za ta nema cimmawa a nan gaba, a kokarin shimfida hanya ga karuwar karfin al'adu daga dukkan fannoni, da kuma karfinsu na yin takara da sauran al'adu.

Amma wasu masana suna ganin cewa, yada al'adun kasar Sin yadda ya kamata, batu ne da ya kamata a warware cikin gaggawa a halin yanzu, in dai ana son samun daidaitaccen matsayin al'adun Sin a tsarin al'adu iri daban daban na duniya, kuma yadda wakar "Gangnam Style" ta kasar Koriya ta Kudu ta samu karbuwa a duk fadin duniya misali ne dake nuna yadda za a iya fitar da kasar Sin daga duhu ta fuskar yada al'adunta.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China