in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin wasu kasashe da jam'iyyun siyasa sun taya Xi Jinping murna
2012-11-16 16:46:47 cri
A ran 15 ga wata, shugabannin wasu kasashe da ma jam'iyyun siyasa daban daban sun gabatar da sakon taya murna ta waya da wasiku ga Xi Jinping, kan matsayin da ya samu na babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 18.

Cikin wadanda suka bayyana sakon taya murnar har da shugaban Amurka Barack Obama, wanda ya ce yana fatan yin hadin gwiwa da takwaransa na Sin, musamman ta fannin karfafa dangantakar abokantaka tsakanin kasashen biyu.

Shi ma shugaban jam'iyyar hadin kan kasar Rasha, kuma firaministan kasar Dmitrii Medvedev, ya aike nasa sakon murna, inda a cikin sakon, Dmitrii Medvedev ya amince da manyan nasarorin da Sin ta samu wajen inganta ayyukan raya kasa, a karkashin jagorancin jam'iyyar Kwaminis ta Sin. Kuma ya yi imanin cewa, ko shakka babu, Sin za ta ci gaba da bunkasa ta hanyar gudanar da kudurorin da aka zartas a yayin babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta Sin karo na 18.

Shugaban kungiyar tarayyar kasashen Afirka na wannan zagaye, kuma shugaban kasar Benin Thomas Yayi Boni ya bayyana a cikin sakonsa cewa, zaben Xi, ya bayyana amincewar jama'ar Sin da jam'iyyar Kwaminis ta kasar, kan kwarewarsa ta jagorar jama'a domin gina wata kasar zamani mai karfi, inda ake tabbatar da dinkuwar kasa waje daya da samun walwala . Bugu da kari, yana fatan a karkashin jagorancin Xi, hadin gwiwar tsakanin kasashen biyu zai ci gaba da inganta.

Shi kuwa a cikin nasa sakon murnar, shugaban jam'iyyar kare dimokuradiyya ta kasar Burundi Pascal Virginia Bangda, cewa ya yi, ya yi imanin cewa dangantakar dake tsakanin jam'iyyar Kwaminis ta Sin da ta sa, za ta ci gaba da karfafa, lamarin da zai amfanawa jam'iyyun da kuma kasashen 2. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China