in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabbin shugabannin kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin sun gana da manema labaru
2012-11-15 18:38:55 cri






A ran 15 ga wata, Beijing ya jawo hankalin dukkan kasashen duniya, sakamakon fitar da sunayen sabbin shugabannin Jam'iyyar Kwaminis ta Kasar Sin ta hanyar zabe. Xi Jinping, sabon daraktan jam'iyyar shi ne ya jagoranci sauran zaunannun mambobi shida na kwamitin tsakiya na jam'iyyar don ganawa da manema labaru na gida da na waje, inda ya nanata cewa, sabuwar hukumar shugabanci ta JKS za ta sauke babban nauyi da ke wuyanta don al'umma, jama'a da kuma jam'iyyar. Tabbas ne za ta nuna kwazo don gamsar da tarihi da kuma jama'a.

A ranar 15 ga wata da safe a nan birnin Beijing, an bude cikakken zama na farko na sabon kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma bayan taron, zababben babban sakatare na kwamitin tsakiya na

jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci sabbin zaunannun wakilan hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin don gana da manema labaru na gida da na waje, da farko dai, Mr. Xi ya gabatar da wadannan sabbin shugabanni ga jama'a, ya ce, "A gun taron zabe ne, aka zabi mambobi 7 na zaunannun wakilan hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma aka zabe ni a matsayin babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar, daga bisani kuma zan gabatar da abokan aikina na zaunannun wakilai 6 gare ku, su ne Li Keqiang, Zhang Dejiang, Yu Zhengsheng, Liu Yunshan, Wang Qishan, Zhang Gaoli."

A cikin sabbin shugabannin kwamitin tsakiya, Xi Jinping da Li Keqiang sun taba rike mukaman zaunannun wakilan hukumar siyasa na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a hukumar siyasa da ta gabata, yayin da sauran mambobi 5, suke a matsayin sabbin mambobi a wannan hukuma.

Bayyanar sabbin zaunannun wakilan kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya jawo hankalin kafofin yada labaru na gida da waje sosai, kafofin yada labaru sun ruwaito yadda yayin ganawarsa da 'yan jaridu a karo na farko, a matsayinsa na babban sakatare na kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ya nanata "Nauyin da ke wuyansu" da kalmar "Jama'a" har sau da dama, ya ce, "Nauyin da ke wuyanmu, shi ne, na tabbatar da hadin gwiwa da shugabanci jama'iyyar kwaminis da jama'a daga kabilu daban daban na wannan kasa, don ci gaba da kokartawa wajen cimma burin farfado da al'ummar kasar Sin.

Nauyin da ke bisa wuyanmu, shi ne, a yi hadin gwiwa da shugabanci jam'iyyar kwaminis da jama'a na kabilu daban daban na kasar, don taimakawa jama'a haye wahalhalun da suke gamuwa da su cikin rayuwarsu, kuma za mu nace bin hanyar samun wadata tare. Kazalika, nauyin da ke bisa wuyanmu shi ne, a yi kokari tare da abokan aiki na jam'iyyar, don daukar kwararran matakai wajen shawo kan matsalolin da ke shafar mu."

Daga cikin takaitaccen bayani game da rayuwar zaunannun wakilan hukumar siyasa ta kwamitin tsakiya ta jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ana ganin cewa, dukkansu sun fito ne daga kananan hukumomi, abin da ya sa sabbin shugabannin kasar ke fahimtar zaman rayuwar jama'a sosai.

A wannan rana, yayin da Xi Jinping ya gana da manema labaru ya jaddada cewa, jama'ar kasar Sin, jama'a ce mai kwarjini a duniya, abin da jama'ar kasar suke sa ran gani a nan gaba shi ne burin da aka saka gaba game da aiki na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Mr. Xi ya ce, "Jama'ar kasar Sin suna kaunar zaman rayuwarsu, kuma suna sa ran samun ilmi da ayyuka masu kyau, da albashi mai kyau, kana da inshora da zamantakewar al'umma mai kyau, kana da samun aikin jinya mai kyau da kyawawan gidajen kwana, kuma suna fatan yaransu za su girma cikin koshin lafiya, da karuwar jin dadin aikinsu da rayuwarsu, haka nan jama'a suna sa rai sosai game da makomar rayuwarsu, abin da ya zama burin da muka sa a gaba a aikinmu."

Haka kuma, A madadin sabbin shugabannin jam'iyyar, Xi Jinping ya bayyana aniyarsu ta kara bude kofa ga waje da yin kwaskwarima a gida, inda ya jaddada cewa, za a ci gaba da wayawar da kai, tare kuma da ci gaba da raya jigon samar da ababen walwala. Hasashen ra'ayin jama'a na nuna cewa, wannan bayani ya sheda niyyar sabbin shugabannin ta kara azama ga bude kofa, ga waje da yin kwaskwarima a gida.(Kande, Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China