in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An gyara kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin
2012-11-14 17:54:50 cri






A ranar 14 ga wata a nan birnin Beijing, an rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, inda aka gyara kundin tsarin jam'iyyar, kuma an maida ra'ayin raya kasa ta kimiyya a matsayin tunanin tushe na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin. Gyararren kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta Sin ya biya bukatun jama'ar kasar bisa halin da ake ciki a yanzu, don haka yana da babbar ma'ana.

A watan Nuwanba a babban dakin taron jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing, an zartas da gyararren kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin wato CPC a gun babban taron wakilan jam'iyyar karo na 18, inda aka maida ra'ayin raya kasa ta kimiyya a matsayin tunanin tushe na jam'iyyar CPC.

Kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tsarin tushe ne ga jam'iyyar. Kuma tunanin tushe da aka tsara a cikin kundin jigo ne ga jam'iyyar yayin da take tsara buri, manufofi da kuma ayyukanta.

An gabatar da ra'ayin raya kasa ta hanyar kimiyya don biyan bukatun jama'a. Yayin da ake samun ci gaban tattalin arziki a kasar Sin ba tare da matsalar rashin abinci ba, jama'ar kasar Sin sun fi maida hankali ga yadda za a dada yawan kudin shiga, da kyautata muhallin kasar.

Wata likita mai suna Xu Ruozuo, tana da wani yaro dake karatu a makarantar firamare, shi ya sa ta sa lura sosai kan yadda za a kyautata tsarin bada ilmi, ta ce, "Mu iyalai da dama muna fatan za a yi kwaskwarima kan tsarin bada ilmi, domin tsarin bada ilmi na kasar Sin na yanzu ya kawo illa ga yaran kasar a fannin kirkire-kirkire da tunanin yin hadin gwiwa. "

Burin jama'a ya bayyana bukatun yin kwaskwarima. Bisa halin da ake ciki a yanzu, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin dake kan karagar mulkin kasar ta maida ra'ayin raya kasa ta kimiyya a matsayin tunanin tushe ta hanyar gyara kundin tsarin jam'iyyar, wannan shi ne babbar nasarar da jam'iyyar ta samu a fannin tunani, kana ya bayyana cewa, jam'iyyar ta tsara manufofi wajen jagorancin jama'ar kasar, don cimma burin inganta zamantakewar al'ummar kasar a dukkan fannoni, tare da biyan bukatun jama'ar kasar a wannan fanni. Wani masani a nan kasar Sin mai suna Cai Zhiqiang ya yi tsokaci yana mai cewa,"Maida ra'ayin raya kasa ta kimiyya a matsayin tunanin tushe na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin yana da nasaba da samar da moriyar ga jama'ar kasar. Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin tana da ikon rarraba albarkatu, kuma burinta shi ne manufofin da ta gabatar su iya biyan bukatun jama'a da kuma kawo karin moriya ga jama'a. Don haka, sabon burin jama'ar kasar shi ne burin jam'iyyar dake kan karagar mulkin kasar."

Wannan gyararren kundin tsarin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, shi ne karo na farko da aka gabatar da ra'ayin wayewar kai ta kiyaye muhallin halittu yayin da ake daukar matakan raya kasa a fannonin tattalin arziki, siyasa, al'adu da kuma zamantakewar al'umma. Kana shi ne muhimmin aiki da zai taimaka wajen aiwatar da ra'ayin raya kasa ta kimiyya. Game da wannan, shugaban kasar Sin Hu Jintao, ya yi alkawari a cikin rahoton da ya gabatar a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 cewa,"Wayewar kai ta kiyaye muhallin halittu yana da nasaba da moriyar jama'a, da kuma makomar al'ummar kasar. Tilas ne a dora muhimmanci kan aikin kiyaye muhalli, da yin kokarin raya kasar Sin, da kuma samun bunkasuwa mai dorewa." (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China