in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
(Sabunta)An rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18
2012-11-14 16:51:03 cri

Yau Laraba 14 ga wata, an rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 cikin nasara.Taron ya yi kira ga dukkan jam'iyyar da su 'yantar da tunani, da yin gyare-gyare a gida, da bude kofa ga kasashen waje, da haye wahalhalun da ke gabanta, da nace bin hanyar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar Sin, don cimma burin zaman wadata daga dukkan fannoni. Haka kuma a cikin rahoton da aka gabatar a yayin taron, an sake jaddada buruka 2 na shekaru dari-dari, wato ya zuwa lokacin da aka cika shekaru 100 da kafa jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, za a cimma burin samun wadata daga dukkan fannoni, yayin da izuwa lokacin zagayowar shekaru 100 da kafa sabuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, za a gina kasar ta zamani mai wadata, demokuradiyya, wayewar kai, kuma mai bin ra'ayin gurguzu kana cikin lumana.

Sharhi na kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua ya nuna cewa, Sin ta fara kidayar ragowar lokaci na cimma burin samun wadata, ya zuwa shekarar 2020, sauran shekaru 8 da wata daya kawai, yanzu, Sin ta shiga wani muhimmin lokaci, na samun wadata daga dukkan fannoni.

Ban da wannan kuma, sharhin ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kara aniyarta ta bin hanyar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar, bugu da kari, ta kara sanin burin da za ta cimma kuma ta kyautata matakan da za a dauka wajen cimma burin yadda ya kamata. Haka kuma, za a raya tattalin arziki, siyasa, al'adu, zamantakewar al'umma, kana da kiyaye muhallin halittu, don cimma burin samun wadata daga dukkan fannoni, da zamanantar da zamantakewar al'umma iri na gurguzu, da raya al'ummar kasar Sin. Haka nan, an yi amfani da ra'ayin raya kasa ta harkokin kimiyya wajen tsara rahoton da aka gabatar a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, wanda ya zayyana harkokin raya tsarin gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China