Sharhi na kamfanin dillancin labaru na kasar Sin Xinhua ya nuna cewa, Sin ta fara kidayar ragowar lokaci na cimma burin samun wadata, ya zuwa shekarar 2020, sauran shekaru 8 da wata daya kawai, yanzu, Sin ta shiga wani muhimmin lokaci, na samun wadata daga dukkan fannoni.
Ban da wannan kuma, sharhin ya ce, jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ta kara aniyarta ta bin hanyar gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar, bugu da kari, ta kara sanin burin da za ta cimma kuma ta kyautata matakan da za a dauka wajen cimma burin yadda ya kamata. Haka kuma, za a raya tattalin arziki, siyasa, al'adu, zamantakewar al'umma, kana da kiyaye muhallin halittu, don cimma burin samun wadata daga dukkan fannoni, da zamanantar da zamantakewar al'umma iri na gurguzu, da raya al'ummar kasar Sin. Haka nan, an yi amfani da ra'ayin raya kasa ta harkokin kimiyya wajen tsara rahoton da aka gabatar a gun babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18, wanda ya zayyana harkokin raya tsarin gurguzu da ke da halayyen musamman na kasar.(Bako)