in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Kenya na sa ido ga hadin gwiwa da sabbin shugabannin JKS
2012-11-14 15:06:41 cri
Kwanan baya, a yayin amsa tambayoyin da wakilin gidan rediyon CRI ya yi masa, mataimakin shugaban kasar Kenya Kalonzo Musyoka ya nuna cewa, yana sa ido ga hadin gwiwa da sabbin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin.

A yayin da ya halarci bikin bude hanyar mota ta Thika, wato babbar hanyar zamani ta farkon a kasar ta Kenya da wani kamfanin Sin ya gina, Kalonzo Musyoka ya ce, "Muna sa ido sosai ga hadin gwiwa da sabbin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin." Ya kuma kara da cewa, a matsayinsa na mataimakin shugaban kasar Kenya, kuma shugaban jam'iyyar bunkasa dimokuradiyya, ya nuna fatan alheri ga sabbin shugabannin jam'iyyar kwaminis ta Sin. Bugu da kari, ana iya ganin cewa, hadin gwiwa da ke tsakanin kasashen biyu zai cigaba da bunkasa tare da samun sakamako mai kyau, kuma bikin kammalar wannan babbar hanya dake karkashin jagowancin shugaban kasar Mwai Kibaki yana dada nuna hakan matuka. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China