in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An fara bikin rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18
2012-11-14 10:52:50 cri

Yau Laraba 14 ga wata da karfe 9 na safe, aka fara bikin rufe babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 a karkashin jagorancin.

Shugaban kasar Sin Mr. Hu Jintao, kuma wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin da yawansu ya kai 2307 da wasu da aka gayyata suke halartar taron.

Aiki na farko na bikin, shi ne zaben kwamitin tsakiya da babban kwamitin ladabtarwa, kuma, an amince sunayen masu sa ido game da zabe, da shugaban masu sa ido game da zaben. Bisa rahoton da shugaban masu sa ido ga zaben ya bayar kan harkokin kuri'un da aka kada, Mr. Hu ya sanar da cewa, bisa ka'idojin zaben, an amince da sakamakon zaben.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China