in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An nuna yabo ga burin da aka gabatar a taron jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin
2012-11-13 20:41:08 cri
A wajen taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da yanzu haka a ke yi a nan birnin Beijing, an gabatar da burin samun walwalar al'ummar kasar a shekarar 2020, gami da shirin kafa 'kasar Sin mai kyan gani', abin da ya janyo yabo daga gamayyar kasa da kasa.

Donald Lewis, masanin ilimin shari'a na jami'ar Stanford dake kasar Amurka, ya ce kasar Sin ta zabi wata sabuwar hanya don raya tattalin arzikinta, wadda ta fi mai da hankali kan nan gaba, tare da dacewa da ra'ayin da gwamnatin kasar ke da shi na raya kasa ta wasu nagartattun hanyoyi. Sannan kuma wasu alamun musamman na wannan tsari su ne raya tattalin arziki tare da kiyaye muhalli, da samun ci gaba mai dorewa. A cewar Mista Lewis, babu wata kasar dake tasowa wadda ta taba sanya wani babban buri kamar haka, don haka idan kasar Sin ta samu cika burinta, to, za ta shiga cikin jerin kasashen da tattalin arzikinsu ke kan gaba a duniya, wadanda suka hada da Amurka da kasashen Turai.

Shi ma a nasa bangare, wani masanin ilimin tattalin arziki na kasar Kenya, kuma tsohon sakataren ma'aikatar zirga-zirgar kasar, Dokta Ikiyala, ya bayyana cewa, cikin batutuwan da ake tattaunawa a kai a babban taron wakilan jam'iyyar Kwaminis ta kasar Sin na wannan karo, ya fi sha'awar ra'ayin da aka dauka na raya kasa ta hanyoyin da suka dace. A cewarsa, wannan manufar ta mai da moriyar jama'a a kan gaba a cikin abubuwan da ake lura da shi yayin da gwamnatin kasar ke tsara manufofinta, kana ta bukaci a yi la'akari da hakikanin yanayin da ake ciki yayin da ake kokarin daidaita matsaloli daban daban, haka zalika inji Dr Ikiyala wannan ra'ayi ya ba da dama domin a kirkiro wasu sabbin dabaru da manufofi. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China