in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin za ta bi sabuwar alkiblar raya harkokin soja na zamani
2012-11-13 18:45:56 cri






A yanzu haka babban taro karo na 18 na wakilan jam'iyyar kwaminis da ke mulki a kasar Sin na gudana a nan birnin Beijing. Bayanin da babban sakataren kwamitin tsakiya na jam'iyyar, HuJintao ya yi kan harkokin tsaro da raya harkokin soja cikin rahoton da ya gabatar a wajen taro ya jawo hankalin bangarori daban daban, wanda ya yi nuni da cewa, za a yi kokarin kammala aikin raya harkokin soja na zamani, domin tabbatar da ganin samun babban ci gaba ta fannin raya harkokin soja na zamani ya zuwa shekarar 2020. Bayan haka, bayanin da ya yi dangane da tsaron teku da sararin samaniya da kuma yanar gizo ta internet duk na daukar hankalin al'umma.

Wei Wenhui shi ne kwamandan wani sashen rundunar sojan ruwa da ke tsaron tekun gabashin kasar Sin, kana wakilin jam'iyyar kwaminis ta kasar a wajen taron wakilan jam'iyyar da ake yi yanzu haka. Tun lokacin da ya fara tukin jirgin sama da ke aiki da farfela a shekarar 1984, har zuwa yanzu da yake tukin jirgin saman yaki na zamani da kasar Sin ta kera da kanta, Wei Wenhui ya gane ma idonsa irin sauye-sauyen da suka faru a harkokin sojojin kasar Sin cikin shekaru 30 da suka wuce ta fannin ci gaban na'urorin soja da kuma harkokin soja na zamani. Yana mai cewa,"Na fara tukin jirgin sama ne a shekarar 1984, kuma idan mun yi magana a kan na'urorin aikin soja, tun lokacin da na fara tukin jirgin sama da ke aiki da farfela har zuwa yau da na ke tukin jirgin saman yaki na zamani da kasarmu ta kera da kanta, wanda abu ne da da ko kadan ban yi tunani zai kasance ba, amma ga shi yanzu ya zamo gaskiya. Cikin shekaru 10 da suka wuce tun bayan taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 16, mun samu babban ci gaba ta fannin raya harkokin soja na zamani, musamman ta fannin tsarin ba da jagoranci, abin da ya ba wa mayakanmu kwarin gwiwa da tallafi wajen tinkarar fada a nan gaba."

Hasali ma dai, furucin da ya shafi harkokin soja na zamani ya fara bullowa ne a shekarar 2003 a tsare-tsaren soja da jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin ke son aiwatarwa, da nufin inganta kwarewar soja ta fannin yin amfani da bayanai bisa fasahohin zamani, a kokarin cimma burin daukaka karfin soja.

A cikin shekarun baya, ba kawai rundunar sojan kasar Sin ta samu babban ci gaba ta fannin raya harkokin samar da bayanai da ci gaban na'urorin aikin soja ba, har ma an samu ci gaban kwarewar sojojin kasar. Dimbin dalibai sun shiga aikin soja bayan da suka kammala karatu daga jami'a, kuma Zhang Ou wanda ke da shekaru 32 da haihuwa na daya daga cikinsu. A shekarar 2001, Zhang Ou ya shiga rundunar soji da ke sarrafa makamai masu linzami ta kasar Sin, wato yau shekaru 11 ke nan yana aikin soja, kuma cikin wadannan shekaru 11 da suka gabata, rundunar da yake ciki ta samu babban ci gaban ta fuskar na'urorin aikin soja na zamani.

Zhang Ou yana ganin cewa, yanzu haka tsarin makamai masu linzami na kara samun inganci, don haka, ya kamata sojoji su kara kokarin koyon ilmin zamani, ta yadda za su iya sarrafa makaman yadda ya kamata. Zhang Ou yana mai cewa,"Tsarin sarrafa makamai masu linzami da muke amfani yanzu ya kara samun inganci, abin da ke bukatar karin kwarewar sojoji ta fannin iya amfani da fasahohi na zamani. Don haka, muna kokarin nazarin fasahohin zamani da inganta kwarewarmu, ta yadda za mu iya sarrafa makamanmu yadda ya kamata.

A cikin rahoton da Hu Jintao ya gabatar a wajen taron jam'iyyar, furucinsa da ya shafi mai da hankali a kan tsaron teku da na sararin samani da kuma na yanar gizo ta internet ya jawo hankalin al'ummar cikin gida da na kasashen waje, kuma ana ganin cewa, a sabili da matsalar teku da kasar Sin ke fuskanta a sassan teku da ke gabashin kasar da na kudancinta, yadda jam'iyyar kwaminis ta kasar ta jaddada hakkinta a kan teku ya shaida cewa, kasar za ta inganta karfin sojan ruwa, a kokarin kiyaye hakkin kasar a kan iyakokin ruwa.

A watan Satumba na wannan shekara, kasar Sin ta fara aiki da jirgin ruwan yaki mai daukar jirgen saman yaki da ya kasance na farko a kasar, wanda ya daukaka karfin sojan ruwa na kasar kwarai da gaske. Mei Wen, jami'in kula da harkokin siyasa a cikin jirgin ya bayyana cewa,"Jirgin ya taimaka sosai ta fannin inganta karfin sojan ruwanmu da kuma karfin tsaron kasarmu, abin da zai taimaka ga kiyaye mulkin kasa da tsaronta da kuma ci gabanta."(Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China