in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An zartas da daftarin takardar jerin sunayen mutane 'yan takara wajen zaben shugabannin JKS
2012-11-13 16:22:05 cri
Yau Talata 13 ga wata da safe, kungiyar shugabanci ta babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta Sin karo na 18 ta kira taro karo na 3 a babban dakin taro na jama'ar kasar Sin dake nan birnin Beijing, inda aka zartas da daftarin takardar jerin sunayen mutane 'yan takara wajen zaben mambobin kwamitin tsakiya na 18, wakilan da ba cikakkun mambobi ba na kwamitin, da mambobin kwamitin ladabtarwa na tsakiya, kuma za a gabatar da wadannan sunayen ga kungiyoyin wakai daban-daban don a tauttauna a kai. Aboki Hu Jintao ya jagoranci wannan taro.

Za a yi zabe a hukunce a ranar gobe 14 ga wata da safe. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China