in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Iraki yana fatan babban taron wakilan JKS karo na 18 zai inganta zaman rayuwar jama'ar Sin
2012-11-13 15:21:53 cri
A daren ran 12 ga wata, a yayin amsa tambayoyin da wakilin gidan rediyon CRI ya yi masa a rubuce, shugaban kasar Iraki kuma shugaban kawancen kishin kasa na Kurdistan na kasar Jalal Talabani ya bayyana cewa, ya mai da hankali sosai kan babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da ake gudanarwa yanzu, kuma yana fatan babban taron zai dada kyautatawa tare da daga zaman rayuwar jama'ar Sin zuwa wani sabon matsayi, kazalika taron zai samar da hanyoyin ciyar da manufofin kasar a fannoni daban daban gaba.

Yayin da yake amsa tambayoyin da aka yi masa, Jalal Talabani ya ce, yana fatan Sin za ta kammala babban taron cikin cikakkiyar nasara, kuma jam'iyyar kwaminis ta Sin za ta iya cigaba da karfafa manufofinta, a fagen gudanar da ayyukanta da za su shafi zamantakewar al'ummar kasar, matakin da zai kai ta ga cimma dukkan alkawuran inganta zaman rayuwar jama'ar kasar zuwa wani sabon matsayi. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China