Game da tsarin yin gyare-gyare a fannonin kiwon lafiya da aka mai da hankali sosai a kai, an ce, yawan al'umma da suka mori inshorar ganin likita sun zarce biliyan 1.3, kuma wannan adadin ya kai kashi 95 cikin 100 na yawan al'ummar kasar, inda a zahiri ake iya ganin ci gaba da Sin ta samu a wannan fanni, amma raguwar matsala ta fi karfi a manyan asibitocin da ke birane, inda ake kashe kudade da dama kuma da wuya ne, a iya ganin likita, baya ga gibi da ke kasancewa tsakanin tsarin ba da inshora game da harkokin lafiya da bukatun jama'a, don haka, nan gaba, za a kokarta wajen warware wannan matsala.
Game da aikin samar da guraben aikin yi, Sin ta cimma burin kara samar da guraben aikin yi ga al'umma, amma tafiyar hawainiyar da aka samu wajen habakar tattalin arziki ya yi tasiri game da aikin samar da guraben aikin yi, game da wannan, nan gaba, za a himmantu wajen samar da kyawawan hanyoyin samar da ayyukan yi ga jama'a, kuma gwamnatin za ta dauki kwararan matakai game hakan.
Kazalika kuma, an gudanar da aikin gina gidaje domin more rayuwar jama'a, a garuruwa da birane yadda ya kamata, haka nan aikin kiyaye muhalli ya samu kyautatuwa, sai dai akwai sauran rina a kaba, game da wannan namijin aiki da gwamnatin ke ci gaba da aiwatarwa.(Bako)