in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta tsaya tsayin daka kan manufar harkokin diplomasiyya ta neman hadin gwiwa da samun moriyar juna
2012-11-12 17:58:23 cri






A cikin rahoton da aka gabatar wa babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 da yanzu haka ake gudanarwa a nan birnin Beijing, jam'iyyar kwaminis ta Sin dake rike da mulkin kasar ta bayyana manufar kasar a nan gaba ta fannonin harkokin cikin gida da na kasashen waje, kamar "inganta kafa wata sabuwar dangantaka tsakaninta da manyan kasashe yadda ya kamata", "kokarta samun bunkasuwa da samar da alheri ga kasashen dake makwabtaka", da sauransu, wadanda suka amsa kulawar da kasashen waje suke nuna wa harkokin diplomasiyya na wannan kasar dake samun saurin sauye-sauye da ci gaba.

"A ganina, wannan batu bai yi tasiri a gare ni ba, saboda mun fahimci sosai." Kalaman Malam Zhang Xun ke nan 'dan shekaru 31 a duniya dake aiki a wani kamfanin Japan dake nan kasar Sin, ya bayyana cewa, takaddamar dake tsakanin kasashen Sin da Japan kan tsibirin Diaoyu ya sanya shi mayar da hankali sosai kan makomar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu a nan gaba, amma a hannu guda kuma ya gaya wa manema labaru cewa, duk da haka dai matsalar ba ta yi wani tasiri ga aikinsa, da yadda yake tare da abokan aikinsa na Japan ba.

"Kasashen Sin da Japan na bukatar juna, ba za su iya samun ci gaba ba idan sun rabu da juna." Inoue Yoichi, shugaban reshen gidan talibijin na TBS na kasar Japan dake nan birnin Beijing, ya gaya wa manema labaru cewa, yana kara yin la'akari da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu sakamakon takaddamar da ta kunno kai dangane da tsibirin Diaoyu.

Kamar yadda Inoue Yoichi yake, batun da ya fi jawo hankalin manema labaru na kasar Japan, wadanda ke ba da labarai game da babban taron wakilai karo na 18 na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin a nan birnin Beijing, ita ce, manufar harkokin diplomasiyya da kasar Sin za ta bi a nan gaba, hakan dai ita ma wani babban batun da manema labaru daga kasashen makwabtaka da Sin suke neman karin haske akai.

A cikin rahoton da aka gabatar a yayin babban taron wakilan, an tabbatar da cewa, kasar Sin za ta yi kokarin neman bunkasuwar kanta tare da samar da alheri ga kasashen dake makwabtaka da ita. Manazarci a cibiyar nazarin manufofi ta kasa da kasa (International Institute for Strategic Studies -- IISS), Gao Zugui yana ganin cewa, hadin gwiwa irin ta samun moriyar juna ta sanya kasar Sin ta kasance aminiyar cinikayya da ta fi girma ga yawancin kasashen dake makwabtaka da ita, ciki har da kasar Japan. Nan gaba kuma, kasar Sin za ta ci gaba da kara azama ga hadin gwiwa da samun nasara tare a shiyyar. Gao ya ce,

"A wadannan shekarun kasar Sin ta samu saurin bunkasuwa ta fuskokin tattalin arziki da zamantakewar al'umma, wannan ya sa aka bullo da wata alamar neman ci gaba bisa bunkasuwar kasar Sin, ba ma kawai an samu alamar a yankunan dake makwabtaka da ita ba, har ma a duk duniya baki daya. Ayyukan da za mu yi a nan gaba shi ne, yadda za mu iya kara samar da alheri ga duniya, ana iya cewa, muna da babbar dama a wannan fannin."

Gardamar ikon mallakar yankuna da ta teku ta kasance wata babbar matsala dake tsakanin kasar Sin da wasu kasashen dake makwabtaka da ita. Mataimakin shugaban jami'ar koyon harkokin diplomasiyya ta kasar Sin, Qin Yaqing ya bayyana cewa,

"A cikin rahoton, mun jaddada kiyaye ikon moriyar yankunan teku, wannan na da muhimmanci sosai. Wannan abu ne da ya kamata ko wace kasar dake da ikon mallaka ke yi. Kazalika rahoton ya nanata cewa, manufar da muke bi ta tsaro, ba ta canja ba. Kasar Sin tana bin hanyar yin shawarwari da tattaunawa don wareware matsalar yankunan kasa, ita ce kuma babban matsayin da take dauka a kowa ne lokaci."

Bugu da kari, a cikin rahoton an tabbatar da "inganta sabuwar dangantaka tsakanin kasar Sin da manyan kasashe yadda ya kamata cikin dogon lokaci", wannan ne karo na farko da aka gabatar da wannan batu cikin rahoton babban taron wakilai na jam'iyyar kwaminis ta kasar. Qin Yaqing ya yi bayani kan sabuwar dangantakar kamar haka,

"Ya ya sabuwar dangantaka ta ke kasancewa tsakanin manyan kasashe, ciki har da manyan kasashe masu ci gaba, da kasashen dake tasowa cikin sauri? Kamata ya yi su warware matsaloli a tsakaninsu ta hanyar lumana da tattaunawa."

Sanin kowa ne cewa, ba za a iya kaucewa sabani da rikici a tsakanin kasashe ba, abin da ya fi muhimmanci shi ne, ta yaya za a magance irin wadannan matsaloli.

Game da takaddamar tsibirin Diaoyu dake tsakanin kasashen Japan da Sin, shugaban gidan talibijin na TBS dake nan birnin Beijing, Inoue Yoichi ya bayyana cewa,

"A matsayinmu na kafar watsa labaru ta kasar Japan, ba za mu jaddada matsayin kasarmu na nuna kiyaya ga kasar Sin ba, batun da ya kamata Japan ta yi la'akari da shi shi ne, yaya za ta kulla dangantakar da ta dace a tsakaninta da Sin, yaya za ta yi mu'ammala da kasar Sin da ke habaka a halin yanzu? Masu iya magana na cewa,wai dabara ta rage ga mai shiga rijiya." (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China