in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin ta sa kaimi ga jarin jama'a ya shiga harkokin bankuna
2012-11-12 17:18:52 cri
A ranar 11 ga wata, an shirya taron manema labaru game da "Aikin yin gyare-gyare ga harkokin banki da raya kasa ta hanyoyin kimiyya" da aka yi a cibiyar yada labaru ta babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, inda wakilin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 18 kuma shugaban kwamitin sa ido game da harkokin bankuna na kasar Sin Shang Fulin ya bayyana cewa, Sin za ta ci gaba da sa kaimi ga tallafawa jarin da jama'a ke sanyawa cikin harkokin bankin kasar.

Shang Fulin ya jaddada cewa, Sin na kira ga masu zuba jari daga sassa daban daban da su shiga harkokin cinikayyar bankuna tare da zaiyyana sharadinta. A watan Mayu na bana, kwamitin sa ido game da hada-hadar kudi na kasar ya sa kaimi ga habakar jarin jama'a musamman wanda ke shiga harkokin bankunan kasar, don nuna goyon baya ga jarin jama'a, da sauran jarurruka, don kawo wani kyakkyawan yanayi game da jarin jama'a ta fuskar kasuwancin zamani.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China